Ba laifin ku bane

Kada ku daura wa kanku laifi

Ya fara kamar kowane rana. Na kwashe lokaci da abokai na a cibiyar al’ummar mu. Munyi nishadi kamar yadda muka saba. Sunyi sha’awar jan rigar dana saka. Naji dadi sosai.

Da karfe hudu na yamma, na kama hanyar gida. Na dauki hanyar dana saba bi. Akwai yan maza biyu a mahadar hanyar. Na sha ganin su a wajan, ba komai bane. Na wuce su na cigaba da tafiya na.

Sai kawai naji tafarkinsu a baya na. Na fara jin wani iri. Zuciyata ya fara bugu. Wani murya a kai na yace na fara gudu! Sai kawai na kama gudu nan take. Amma bani da sauri. Hannaye biyu suka kama ni. Na juya nayi fargaba. Naga cewa yan mazan nan biyu ne na mahadar hanyar!

Nayi kokari na kauce, amma sun fi ni karfi. Har suka yaga mun riga na! Da dukka karfi na, na buga daya daga cikin su a gaba. Yayi ihu ya sake ni. Ihun ya jawo hankalin dayan yaron, sai na samu na kauce nayi gudu.

Na koma cibiyar al’ummar mu. Abokai na suka yi gigitawa da suka gan ni. Ina ta nunfashi da karfi, na kasa magana. A karshe, na gaya musu komai. Muka yi sauri mu kai mahadar hanyar, amma yan mazan sun tafi.

Wasu mutane na wucewa. Suka tambaye mu mai ya faru, sai muka gaya musu abun daya faru. Wani mutum ya tambaye ni ko na taba sanin wata yarinya dake saka jan kaya da bata neman fada. Daya kuma yace dana gaida yan mazan, da basu farmaki ni ba. Wata mata tace dana zauna a gida na karanta takarda na.

Naji kunya kuma na bawa kaina laifi. Dana sani na saka kaya mara launi. Dana sani na gaida yan mazan. Laifi na ne.

A gida, na kasa yin wa iyaye na magana. Ina ta bakin ciki gaba dayan ranar. Da safe, mahaifiyata da tambaye ni mai ke damu na. Na fara kuka na gaya mata abun daya faru. Ta lallabe ni kuma ta fahimce al’amarin. Amma tayi haushi da taji abun da mutanen nan suka fadi! Ta gaya mun ba laifi na bane, tace kada na sake na bawa kai na laifin halayyar sauran mutane. Tace wadannan yan mazan sun so suyi mun lahani ne kuma wannan bai shafe abun dana saka ba ko kuwa abun dana ce. Kuma ta fadi dukka abubuwan dana yi sun dace, kamar saurarar muryan nan a cikin kai na daya ce nayi gudu, kuma tace nayi abu mai kyau dana kai rahoton wannan al’amari, kuma bai kamata ayi shiru idan abu kamar haka ya faru ba. Hankali na ya kaunta.

Mahaifiyata ta gaya wa mahaifina abun daya faru. Ya kai rahoto a wajan hukumar ungwan mu, yanzu haka suna neman yan mazan nan.

Da farko, na so na daina zuwa cibiyar al’ummar. Amma iyaye na suka ce kada nayi haka. Na cigaba da kwashe lokaci da abokai na kuma ina yin abubuwar da nake kauna. Bazan bar kowa ko wani abu ya saka ni bakin ciki ba. Na tsira. Ina da karfi.

Idan kun taba samun kanku a wani al’amari kamar Zina, dan Allah kada ku bawa kanku laifi. Baku da alhakin halayyar sauran mutane. Idan kuna so, zaku iya yin magana da wata ko wani amintaccen babban mutum kamar yar uwar ku, ko Innar ku, ko kawun ku– harda iyayen ku kamar yadda Zina tayi.

Kun san wata da irin wannan labarin? Ku gaya mana a sashin sharhi.

Share your feedback