Ba komai idan kika yi dariya a lokacin da kika kunyatar da kanki
Kin taba faduwa a kasa a gaban kungiyar mutane? Kin kwanta a kasa kina kuka? Kwarai a’a, kin tashi nan take. Koda kin kunyata a lokacin, mai yiwuwa kinyi dariya daga baya.
Kamar Hlima.
Halima taje wajan biki da mahaifiyarta. Ta tashi ta naima musu abinci. Lokacin ne mahafiyarta ta lura cewa tana da katon dattin jini a kujeran da take zama.
Halima tana ta kuka da mahaifiyarta take taimakon ta wanke jikin ta a shadda. Taji kunya sosai. Ta kasa yarda cewa duka mutanen dake wajan sun ganta haka. Taji kamar kasa ya bude ya hadiye ta.
Mahaifiyarta ta fara mata wasa akan yadda take kuka kamar karamar yarinya. Suka kwashe dariyan al’amarin da take. Halima ma na wasa akan yadda ta kurkure shinkafan bikin dan dattin kayan ta.
Sai mahaifiyar Halima ta koya mata yadda zata kirga ranakun al’adan ta na nan gaba saboda ta kauce irin wannan al’amarin.
Ba komai bane idan kika kunyata kanki ko kika yi kuskure. Abun muhimmancin shine, yadda kika tashi bayan fadiwan. Yin dariya akan abun da ya faru na taimako. kuma, ki tabata kin koya daga kuskuren ki. Dan haka baza ki kara maimaita kuskuren ba.
Kamar Halim, idan kika samu kanki a wani al’amari mai kunyatar daki kiyi kokari kada ki sa ya dame ki. Ba zai dade ba. Ki koya ganin hasken al’amari koda al’amarin maras kyau ne.
Ki gaya mana akan lokacin nan da kika ga abun dariya a al’amari mara kyau a shafin sharhin mu.
Share your feedback