A kyale ni

A’a na nufin a’a

Shekarun Dupe goma sha shida da ta shiga kungiyar waka a cocin al’ummar su. Tana gwaji kowane rana da sauran yan mata a ungwan su.

Suna gudanarwa a taron makaranta, ko na al’umma, harda bukukuwa.

Tana kaunar kungiyar wakar. Tayi abokan arziki a wajan. Kowane rana tana gaugawar zuwa gwaji. Kowa na kaunar ta, harda Mr Ayo, shugaban kungiyar wakar su.

Mr Ayo nada hankali. Dukka yan matan na kaunar yadda yake koyar da su.

Amma Mr Ayo na kaunar Dupe fiye da sauran yan matan. Wasu lokaci yana daukan ta a motar sa ya kai ta gida.

Yana siyo mata lemun kwalba da abun ciye-ciye wasu lokuta. Koda yaushe yana yabon ta. Ya gaya mata cewa ita budurwa ce mai hikima. Ya ce mata tana da kyau.

Wasu yan matan sun lura yadda yake maida hankali da ita. Suna kiran ta karamar matar Mr Ayo.

Bata damu ba sanda Mr Ayo ya siyo mata wani sarka. Ya gaya mata yana son ta sosai. Yace mata yana son yafi fiye da shugaban kungiyar wakar ta.

Wannan ya bata tsoro. Bata san wanda zata yi magana da ba. Tana jin tsoron gaya wa mahaifiyar ta.

Ta gaya wa yar uwar ta babba. Yar uwarta ta gaya mata tace mishi a’a.

Ta gaya mata tayi hankali. Tace halayyar Mr Ayo bai dace ba. Bai kamata babban namiji yayi amfani da kudi domin yaja hankalin yan mata ba. Ba dukka tsofofin maza dake da hankali wa yan mata ke son wani abu daban daga wajan su ba. Amma akwai wasu kamar Mr Ayo dake bukaci soyayya a musayar kyaututtuka da kuma kudin su.

Ta gaya mata ta daina karban kyaututtuka daga wajan sa. Kuma ta gaya mata ta daina shigan motar sa.

Dupe taji tsoron gaya wa Mr Ayo a’a. Tana tsoro zai yi mata ihu ko kuwa ya kore ta daga kungiyar wakar. Ta tambaye yar uwarta ta taimake ta.

Yar uwarta ta kai karar sa a wajan shugaban al’ummar su. Aka yi wa Mr Ayo kashedi.

Yau Dupe ta dawo kungiyar wakar. Mr Ayo ya daina matsa mata.

Kuna nan kamar Dupe? Akwai wani tsohon mutum dake kokarin samun hankalin ku? Akwai wani daya alkawarin kai ku kasar waje ko kuwa biyar kudin makaranta ku idan kuka yarda kuyi soyayya dasu?

Kuyi mana magana akan sa a wajan sharhi.

Share your feedback