Neman yancin kai
Mahaifiya ta da mahaifi na na kokarin aiki sosai domin su bawa ni da yan uwa na mata guda biyu rayuwa mai kyau. Ina girmama wannan.
Mahaifiya ta na nan a shagon ta da fitowar rana a kowane safe. Mahaifi na na aiki a wani ofishi. Yana barin gida yaje aiki kafan fitowar rana kowane rana.
Wannan ya koya mun darajan aiki da kuma samun kudi.
Na gaya wa yan uwa na ba sai mun riga tambayan akan komai ba. Wasu lokuta zamu iya yin aiki sosai kamar su domin mu samu kudin mu.
Na tuna naga wani atamfa. Yana da kyau sosai. Amma bana son na tambaye mahaifiya ta kudin. Ina son na siyo wa kaina. Haka na fara siyar da zobo a makaranta.
Yar uwar mahaifiya ta na yin zobo mai dadi. Na tambaye ta idan zan iya kai makaranta na siyar.
Bayan da ta koya mun yadda zan siyar dasu, ta bani kwalabe goma.
Da safen nan a makaranta, na siyar dasu. Sai na kara yin haka a rana na gaba. Da ranan daya biyo. A mako na gaba na tambaye yar uwar mahaifiya ta idan zan iya samun kwalabe ishirin a maimakon goma. Na siyar da dukka ishirin.
Sa’an nan da ranar yazo. Nayi tattaki da alfahari naje wajan mahaifiya ta na gaya mata cewa ina son na siya atamfa da kudi na.
Nayi alfahari da kaina. Na tabbatar cewa zan iya aiki kuma na biya bukata na, kamar mahaifiya ta da mahaifi na.
Duk in da naje a rayuwa, Zanyi tunanin wancan atamfan. Zan tuna cewa duk abun da kike so a rayuwa-- koda babba ne ko karami---dole kiyi aiki domin ki same sa.
Menene wasu abubuwa da zaki iya yi domin ki samu kudi ba tare da matsala ba? Gaya mana a shafin sharhin mu.
Share your feedback