Mama, kin san mene?

Yadda Hauwa ta gaya wa mahaifiyarta akan al’adan ta

Tunanin ku (5)

Wata rana, ina zama ina labari da abokai na. Sai kawai naji ba daidai ba. Dana kalla kasa kawai sai naga jini a wajan da nake zaune. Tsoro ya kama ni! Ban san mai ke faruwa ba. Na ji wa kaina ciwo ne?

Bana son na tashi. Kunya ya kama ni. Har na fara kuka. Babba kawata taga cewa bana jin dadi. Sai ta matso kusa dani ta tambayeni meke faruwa. Sai na kasha murya nace “Rukayat, ina ganin zan mutu!”

Dana nuna mata jinin. Sai tace na kwantar da hankalina na daina kuka. Tace ba komai bane, yana faruwa. Tace ya faru da ita da wasu kawayen mu. Tace na gaya wa mahaifiya ta tun yanzu.

Na gaya wa mahaifiya ta? Akan jinin dake fitowa daga can kasa? Toh idan nice sanadin wannan abun fa? Ina tsoro zata mun duka. Rukayat tace mahaifiyata zata fahimta. Wai mahaifiyata ma na yin irin wannan abun a ko wanda wata. Tace mahaifiyata zata mun bayanin komai.

Da mahaifiyata ta kai gida, ina kan jin tsoro. Ban san yadda zan gaya mata ba. Tana dafa abinci a mafada. Ina ta tagumi, na kasa zama waje daya. Zan shiga na fita ban iya cewa komai ba. A karshe, sai ta tambaye ni meke damuna.

Na ja nunfashi dan samun karfin magana. Sai na gaya mata. Bata ji haushi ba. Ta rungume ni tace na fara zama mace. Ta nuna mun yadda zanyi amfani da audugan al’ada. Sai ta zaunan dani ta mun bayanin komai.

Tace ana kiran sa jinin haila. Yana nufi cewa jiki na ya balaga isashshe da zan iya haihuwa. Kuma zan ga wanan jinin a ko wanda wata. Tace ba komai bane, dan haka kada naji tsoro ko naji kunya.

Mahaifiyata tayi murna dana je wajan ta da abu mai muhimmanci haka. Na samu kwanciyar hankali kuma naji dadi dana mata magana. Yin magana da mahaifiyarki ko wata babba da kika yarda da zai taimake ki. Zaki iya koyi abubuwa daga wajan su.

Wa kika gaya wa lokacin da kika fara al’adan ki? ki gaya mana shafin sharhin mu.

Share your feedback

Tunanin ku

Babata

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Na gayawa mahaifiyata

March 20, 2022, 8:04 p.m.

Hmm gaskiya nima naji kunya

March 20, 2022, 8:03 p.m.

Alale

March 20, 2022, 8:03 p.m.

Mamata Nagaya Wa

March 20, 2022, 8:01 p.m.