Yadda zaku bi da matsalolin ku na samari
Ina aji uku a makarantar sekandare dana fara fita da saurayi na. Yana da tsawo, da haske da kuma kyau, wannan ya saka ni son shi. Amma ya ci da gumin son da nake masa.
Ina kaunar sa kuma na amince da shi. Mun kwashe shekara daya tare kafan ya fara nuna asalin halayyar sa.
Ya fara da hana ni sakewa da wasu irin bukatun sa. Yana son muna zuwa yin ninkaya ko kuwa liyafan cin abinci mu kade. Wani lokaci ya tambaya muyi wanka tare. Wani lokaci kuma yace muje wurin rairayin bakin teku ko kuwa wani waje dake da nesa da mutane domin muyi labari.
Abu mai kyau shine iyaye na sun koya mun yadda zan san abun daya dace da kuma wanda bai dace ba. Nace a’a wa dukkan bukatun sa.
Yace mutane shekarun mu na yin dukkan abubuwan da yake tambaya na. Yace babu komai a cikin sa. Yace ba komai idan naje wadannan wajajen dashi.
Sai ya tambaya ko zai iya zuwa ziyarta ni a gida. Na yarda. Da yazo gida ya fara nuna wasu irin halayye. Yaso ya taba hanuna. Na gaya masa ya daina, amma yaki ya saurarre ni. Sai na gaya masa cewa addini na da kuma al’ada na ya hana irin wadannan halayyen. Yayi haushi, ya cire hannun sa sai ya tafi gida.
Na gaya wa babban yaya na abun daya faru. Tace nayi abu mai kyau. Ta tunatar dani akan abun da iyayen mu suka fadi akan samari dake son taba yan mata. Iyaye na sun ce samari kamar haka basu da gaskiya.
A lokacin da nake magana da yar uwa ta saurayi na ya kira ni. Ya nema gafarta akan halayyen sa. Yace yayi kuskure. Sai na hakura. Na karbe shi.
Abubuwa sun koma daidai har sai da wata abokiyata ta ziyarci ni. Da muke duba hotuna a waya na taga hoton saurayi na. Ta tambaye ni ko shi waye ne sai na gaya mata akan sa. Ta gaya mun na barshi tun da wuri. Ta gaya mun akan budurwan sa dabam-dabam. Yadda ya wulakanta yan mata kamar ni. Tace zai lalata rayuwa na. Ta roke ni nayi tunani akan abun data gaya mun.
Na kasa yarda da abokiya na. Na gaya wa yar uwa ta abubuwan data fadi. Yar uwata ta tunatar dani akan shawarar da iyayen mu suka bamu akan samari. A lokacin ne na san cewa zan bar sa.
Na fara gujen sa kadan kadan. Na rage tadi dashi a waya. Na canza masa. Ya lura da halayye sai ya tambaye ni ko akwai abu. Amma nace masa ba komai.
Bayan lokaci kadan na daina magana dashi gabadaya. Kawai na kasa yarda dashi kuma. Duk da cewa yayi kama da wani mai hankali, kawai na san cewa bai dace mun ba.
Yayi kokari muka dawo tare. Wata rana ya kira ni ya tambaya ko zai iya zuwa gani na. Na yarda. Daya zo, ya kawo kyatuttuka, na ki karba. Yaso ya san abun daya faru tsakanin mu. Na gaya masa bana son na fita dashi kuma.
Da farko ya yarda mu rubu. Amma sai ya fara gaya mun abubuwa masu zalunci. Yace daman ba so na yake ba, daya bar ni tun da dadewa.
Wannan bai dame ni ba saboda ina farin ciki bai cimma manufar sa ya lalata ni ba. A wannan lokacin na ga asalin halin sa. Idanu na sun bude. Wannan yaron ne ya hana ni gaya wa iyaye na abubuwa.
Yanzu na koma gaya wa iyaye na abubuwa. Tun lokacin suka koya mun akan maza da kuma abubuwan da zasu iya yi. An cece ni kuma ina farin ciki.
Shawara na wa yan mata dake soyayya shine su koya bidar shawara daga wani babban amintaccen mutum dake kusa dasu. Kada suji tsoron cewa a’a wa kowane roko da basu yarda da ba daga masoyan su.
Share your feedback