Dan uwana Zaina

Ta cancanci rayuwa mafi kyau

``Ilimi – ba aure ba – shi ne kyawun zuba jari za mu iya yi a ciki yan mata a nan gaba” - Malala Yousafzai

Zainab da ni abokai ne. Muna zuwa makaranta tare, wasa da juna tare, mu nayi komai tare. Wasu mutane a makaranta mu na tunanin sewa wai mu tagwaye ne. Muyi wasa da tunani su.

Wani safiya, Zainab ta gaya mun wai iyayenta sun janye ta daga makaranta. Abubuwa sun dame, kuma ba za su iya biyan kudin makarantar ba. Sun ce a shekara ta goma sha uku, ta tsufa don fara taimaka musu kuma wata hanya ta taimakawa ita ce ta aure, mijinta mai arziki. A gaskiya ma, sun riga sun shirya aurenta da wani malam da suna kimza, wani mai kudi a kasuwa garinmu. Ba iya yarda da shi ba.

Zainab tayi magana game da guduwa daga gida - amma zuwa ina? Da ta zauna tare da mu, amma mahaifiyata ba za ta iya ba. Bugu da ƙari, Zainab bata son tayi abun da zai bata ma iyayenta zuciya ba. Labari na tsawon lokaci, shi ne ta yadda da shawara su.

Bayan bikin auren Zainab, ta ci gaba da karatunta. Ba ta so ta yi watsi da mafarkinta na zama masanin kimiyya. Ina raba takardun darasi tare da ita kuma na ba ta takardun litattafai.

Sai ta haifi jaririnta na farko. Bayan haifuwa ta sami wani matsala mai tsanani. bata iya tashi daga gado.

Bai daɗewa ba, mahaifiyata ta motsa ni zuwa wani makaranta gida. Ta so ni in mayar da hankalinna a wasan karshe. Lokaci da na tafi, Zainab ta samu lafiya kuma ta sake yin ciki. A wannan lokaci, ta haifi yan tagwaye. A wannan lokaci, ta dakatar da karatun gaba daya. Tsakanin kulawa da yara da gidanta, ba ta samu lokacin yin wani abu kuma ba.

Lokacin da na fara karatun lissafi a jamia, Zainab ta bude shago na sayar da su biscuits, sabulu da wasu abubuwa kadan.

Ranar da na hadu da ita, Na lura Zainab tana da wani tafiya tare da wata ƙananan matsala - saboda waɗannan rikitarwa a lokacin da ta fara haihuwa. Na yi ƙoƙari na yi magana da ita, amma akwai gagarumar sauti.

Yanzu ina bautan kasa a cikin wani babban kamfani na lissafin kuɗi. Lokacin da na tafi gida don Kirsimeti, sai na hadu da Zinab a kasuwa. Bata da kyau gani da kuma tayarwa, tare da zoben duhu a idanunta. Mun yi gesuwa ga juna, sai; a nan kuma muka bi hanyoyi dabam-dabam, kamar baƙi.

*

Yane kuka ji yandda Zainab da Dan uwan ta basu samu sa`a guda ba? Muyi Magana sa a sharhi sassan.

Share your feedback