Iyali na baza su iya daukan nau’in tura ni makaranta ba

Me zan iya yi?

Sannu Babban Yaya,

A watani da suka wuce iyaye na suka cire ni daga makaranta. Sun ce basu da karfin tura ni makaranta kuma.

Nayi bakin cikin jin cewa bazan iya koma makaranta ba kuma. Tun dana bar makaranta bana komai sai kwashe lokaci ina taimakon maihaifiyata a shagon ta, ko kuwa na lura da kanne na. Ina son karin abubuwa wa kaina. Ina son na zama kama manyan matan nan da nake gani a talabijin.

Ina son na samu daman tura nawa yaran makaranta.

Me zan iya yi domin na tabbata cewa na samu rayuwa mai inganci?

Tare da damuwa sosai,

Halima.


Sannu Halima,

. Nayi bakin cikin jin batun makarantar ki. Yana da kyau da kika san cewa kina son ki koya wasu hanyoyin cin nasara koda baki makaranta.

Na farko, kiyi tunanin wani abu da kike son yi ko kuwa zaki so kiyi. Yin burodi ne, ko gyaran abubuwa, ko kuwa girken abinci, da sauran su.

Na biyu, ki duba kusa dake ki ga ko akwai wani waje ko kuwa wani dake yin wani abu da kike so ko kuwa zaki so kiyi. Ki tambaye su su koya miki. Ki tabbata zaki iya yarda da mutumin. Ko kuwa, zaki iya tambayen iyayen ki suyi musu magana. Ko kuwa ki saka wata/wani amintaccen babba kamar Innar ki ko kawun ki su taimake ki yin musu magana su koya miki.

Kuma zaki iya yin binciken cibiyar fasaha na gwamnati ko kuwa kungiyoyi kusa da ke dake koyar da mutane a kyauta ko kuwa da arha.

Kuma zaki iya koyan kwarewa da yawa a shafin yanar gizo gizo kamar yadda ake adon fuska, ko yadda ake gyara waya, ko kuwa yadda zaki zama mai zane zane, da sauran su. Ki bincika a google akan bayanan komai da kike son ki koya. Ki karanta makalar mu akan yadda zaki yi bincike a shafin yanar gizo gizo

Na karshe, da zaran kin fara shakuwa da horar ki. Ki koya duke abun da zaki iya. Idan kina ji kamar kin koya abubuwa sosai kuma kin kware, zaki iya yin amfani da kwarewar ki ki fara wani kasuwanci.

Idan kika yi ajiyar kudin nan, wa ya sanni, mai yiwuwa ki iya biyan kudin makarantar a nan gaba. Kuma mai yiwuwa ki iya lura da kanki da kuma iyalin ki.

Halima, kiyi setin wani muradi kuma kiyi kokarin cimma burin ki.

Da kyauna,

Babban Yaya.

Share your feedback