Mahaifiyar abokiyata ta hadu

Manya basu bace ba

Sanda Doris tace mahaifiyarta tana son ta hadu da ni, zuciyata ya fara bugu. Eh, na shaku da doris sosai, amma akwai wani abu da bata sani ba game da ni. Ina tsoron manya. Wato ina nufin, tsoro sosai. Basu da fara’a - musamman wa “kananan yan mata”.

Shiyasa dana fara ziyarta gidan Doris, nayi mamaki da mahaifiyarta ta rungume ni. Na kasa motsi. Sai na warware na rungume ta. Sai naji Kamar ina rungumar wata abokiyata dana dade ban gani ba. Doris ta kale mu da murmushi kamar ita ta shirya abun.

Nayi ta yin magana kuma mahaifiyar Doris ta saurarre ni. Na gaya mata akai na, iyali na da kuma safga na. Ashe ita ma tana son yin zane da fensir. Tayi sha’awar zane-zane na kuma ta karfafa ni na cigaba. Bata bi dani kamar karamar yarinya ba. Har ta tambaye ni ko ina sha’awar wani yaro! Abun mamaki!

Na fara sa idon zuwa gidan su Doris. Har take mun tsiya wai bana samun lokacin ta kuma. Gaskiyar shine, na shaku da mahaifiyarta. Bata yi kamar sauran manya dana sani. Har da nawa mahaifiyar. Ina jin dadin yin magana da mahaifiyarta. Amma bana iya yin mata magana akan samari da sauran abubuwa daya shafi yan mata. Ina ganin kamar zata hukunta ni ko kuwa tayi mun fada.

Mahaifiyar Doris kuma dabam take. Duk sanda nayi shiru ko ina jin kunya, tana tunatar dani nayi magana. Duk sanda nayi korafi akan cewa nonuwa na sunyi kanana, tana fadin cewa jikuna dabam ne. Da yake ta hadu sosai sai na yanke shawara na bawa sauran manya dama. A haka na fara yin wa mahaifiyata magana. Na lura cewa bata da zafi da kuma yin hukunta. A gaskiya, ita ma ta taba masaniyar al’amurrar da nake fama da yanzu. Saboda haka ta zama wanda ya dace nayi wa magana.

Kwanakin nan mahaifiyata da ni na shakuwa sosai. Na kosa na gabatar da ita wa mahaifiyar Doris. Wa ya sani? Mai yiwuwa su zama abokai sosai. Mai yiwuwa dukkan mu hudu mu kwashe lokaci tare. Zamu zama kungiya mafu kyau.

* Kun san wasu manya dake da hankali? Meye kuka fi so game da su? Ku gaya mana a nan kasa.

Share your feedback