Shirya, yi seti, lasta: Zaku iya zama mai baiwar kwamfuta na gaba

Labarin Idara mai ban mamaki

Tunanin ku (1)

Wasu shekaru da suka wuce, aka fara wani makarantar manhaja a cibiyar al’ummar mu. Naji kamar na fashe da murna. Ina son kwamfuta sosai.

Bayan ranar haihuwa ta na goma sha uku, iyaye na suka yi mun rijista a wani makaranta. A aji na na farko, wata mallamar mu mai ado ta saka mu gabatar da junan mu. Ina ta jin kunya sosai har nayi kuskuren kiran suna na.

Daga baya,ta gaya mana cewa ana iya kiran manhaja yin coding.

Tayi mana bayani cewa yana nufin bada wa wani kwamfuta umarni tayi wasu abubuwa. Tace yin coding na taimakon mu kirkira aikace-aikace da kuma shafin yanar gizo gizo. Tayi tambaya idan mun san kowane harshen manhaja. Na sani, amma kalmomin sun makale a makogwaro na. Wani yaro ya daga hanun sa sai ya ambata JavaScript. Kowane yaro ya tafa masa hanu.

A mako na gaba, Muka fara koyan yadda ake yin coding. An raba mu a cikin tawaga. Mun rubuta codes wa abubuwa da yawa masu sha’awa.

Da na cigaba da kara koyo, na fara samun aminta yin magana. Na fara tambaya da amsa tambayoyi a aji. Na daina jin tsoron daga hanu a aji. Wannan saboda nayi gwajin amsa tambayoyi a gaban madubi a gida. Kuma na tabbata cewa nayi karatu a gida saboda na san amsan tambayoyin.

Nayi mafarkin kirkira wani aikace-aikacen tsira wa yan mata a al’ummar mu. Dana gaya wa yan tawagar mu, sun kasance da farin ciki su taimake ni.

Aikace-aikacen yayi aiki a hanya mai sauki. Idan kowane dage cikin mu na cikin wani matsala, zamu taba allon wayan mu domin muyi wa mai gadin makarantar mu ishara, domin ya zo ya taimake mu. Kowane mai gadi nada waya da GPS domin ya taimaka lura da mu da sauki.

Bayan da aka gabatar dashi, dukkan makarantar suna ta yabo na. Mutanen da ban taba magana da ba suka zo suna mun barka. Na san cewa ba zan daina coding ba.

Wata rana zan zama injiniyan kwamfuta. Zan so na fara nawa masana’antar– wanda zai canza duniya kamar Google. Na kosa naga yadda rayuwa ta na gaba zai kasance.

Kowa zai iya zama mai baiwan kwamfuta. Idan kuna jin dadin koyon sabobin abubuwa, zaku iya yin banbanci kamar Idara. Koda aikin kafinta, ko Injiniya, ko kuwa mallamar koyarwa, babu abun da baza ku iya yi ba idan kuka saka rai.

Kuna da wani kwarewa da kuke so ku bunkasa? Gaya mana a nan kasa.

Share your feedback

Tunanin ku

Life

March 20, 2022, 7:59 p.m.