Labarin rabuwar Banke da saurayin ta
A watani biyu da suka wuce, Banke ta rabu da saurayin ta. Bata taba tsammanin rana kamar haka zai zo ba.
Soyayyen su nada kyau. Amma akwai matsala daya.
Yana son suyi jima’i. Banke kuma bata shirya yi ba.
Tana son ta jira. Bata son ta dauke ciki. Kuma taji labarin yan mata da suka dauke cuta daga yin jima’i. Banke tana ji kamar bata kai shekarun da zata fara fama da dukkan abubuwa dake zuwa da jima’i.
Ta gaya mishi yadda take ji. Amma ya gaya mata kada ta damu. Yace sauran abokan su nayi. Kuma idan tana kaunar sa, zata yi.
Banke ta tsaya da gaske, tace zata jira.
Ta rikice kuma tana neman wani da zata iya yin wa magana. Sai tayi wa yar uwarta babba magana.
Yar uwarta ta bata shawara mai kyau:
“Banke, idan yazo akan jima’i ke kadai ce zaki iya yanke shawarar lokacin daya dace miki. Kiyi tunanin abubuwan da zasu iya faruwa idan kika yanke shawara cewa baza ki jira ba. Zaki iya karanta wannan makalar akan daukan ciki yanzu domin ki kara sani"
"Kin shirya yin dukka wannan? Idan baki shirya ba, yakamata saurayin ki ya girmama ra’ayin ki. Kada ki bari wani ya matsa miki lamba kiyi wani abu da baki son yi."
"Kin sani, yin jima’i ba shi kadai bane hanyar da zaki iya nuna kauna. Goyon baya, rubuta wasikar kauna, ko kuwa taimakon saurayin ki idan yana bukata, hanyoyi ne da zaki iya nuna kauna. Saurayin ki na bukatan sanin wannan. Kuma, idan yana son ki da gaske, zai jira. Amma, idan ba zai iya jira ba, mai yiwuwa ba shi bane mafi alheri miki. Na san zai iya yin miki wuya ki bar shi, amma yafi ki samu wani dake kaunar ki sosai da har zai jira”
Banke ta san cewa Yar uwarta na fadin gaskiya ne. Bata son saurayi da zai takura mata tayi wani abu da bata so. Tana son wani da zai amince da dabi’un ta. Tayi dogon zance da saurayin ta. Yana ta nacewa wai lokaci ya kai da zasu yi jima’i. Sai Banke ta yanke shawarar rabuwa dashi. Abun da wuya, amma ta san cewa abun daya dace kenan.
Kun taba rabuwa da wani? Zaku iya gaya mana dalilin da kuma yadda kuka yi a sashin sharhi? Sauran yan Springster zasu iya koya daga labarin ku.
Share your feedback