Tambayoyi da amsa na Springster

Menene canjin Springster a gurin ki

Meyasa sunan ya canza zuwa springster?
Mun nema suna da zai sa yan matan su suji kamar suma suna cikin kungiyar- Kungiyar Springster! Yanzu zamu iya cewa “Sannu Springster” wa juna kamar yadda zaku cigaba da hade da babban ‘yar uwa da kuma sauran yan mata a sabon, ingantacen manhajar.

Menene zai canza idan Springster ya fara?
Dukka abubuwan da kika saba da kuma kike so zasu cigaba yadda suke harda labarai, zabe zabe da kuma takara. A bugu da kari, shafin yanar gizo gizon zai kara zama wajan hulda tsakanin yan mata da kuma sha’awa da karin gasar amsa tambayoyi da kuma makala mai tambayoyi da amsa wa kusan dukka tambayoyin ku, babban ‘yar uwa ta san kuna nada su da yawa!
Takaran kalmomin ki na kowane wata zai cigaba kamar yadda aka saba dan ki cigaba da turo amsar ki domin ki samu damar cin nasara samun ladar katin waya.

Akwai abun da nake bukatan yi domin na cigaba da karanta labaran a yanar gizo gizo?
Babu komai, zaki iya cigaba da samun damar amfani da shafin yanar gizo gizon kamar yadda kika saba. Mahada na yanzu na wannan shafin yanar gizo gizo zai tura ki zuwa sabon shafin yanar gizo gizon domin ki cigaba da amfani dashi kamar yadda kika saba. Abun da muke bukata daga gurin ki shine ki cika karin bayanin ki idan wannan siffar ya fara aiki. Amma yin wannan ra’ayin ki ne, zaki iya yanke shawara kada kiyi.

Ina bukatar koma wani manhajar ko shafin yanar gizo gizo?
A’a, ba sai kinyi ba. Kamar yadda na bayyana a tambaya na karke, zaki iya cigaba da amfani da shafin yanar gizo gizon kamar yadda kika saba. Dukka canji zasu zama sabuntar sabon shafin yanar gizo gizon ne.

Yaushe ne wadannan canjin zasu fara?
Wannan shafin yanar gizo gizon zai fara canjn zuwa sabon tsarin Springster daga 26th ga watan Yuni, 2017. Yana nufi cewa wannan shafin yanar gizo gizon zai canza kamani daga mako na gaba. Muna fatan kuna murnar akan sabon Springster kamar yadda muke murna!

Kina da karin tambayoyi ko shawara akan canjin da yazo Springster? Ko kuna da sabobin ra’ayi ma irin makalar da kuke so ku ringa gani a wannan shafin yanar gizo gizon? Dan Allah ki gaya mana a shafin sharhin a nan kasa.

Share your feedback