Kuna fara al'adae ku na farko?

Yadda na bi da al’adana na farko

Ku karanta labarin Farida akan yadda ta bi da al’adar ta na farko.

Shekaru na goma sha daya dana fara al’ada na. Ya fara da ciwon ciki. Nayi wa yan uwa na biyu mata magana, shekarun su goma sha shida da kuma sha hudu. Daya daga cikin su ta bani wani magani. Tace zai taimaka rage zafin ciwon.

Bayan nan suka fara mun tsiya suna mun dariya. Zasu jawo rigar na su tambaye ni menene matsalar sa, wannan zai kara saka ni ji kamar rigar yayi datti da jini. Bai taimaka ba da dan uwan na namiji na gidan mu a ranar.

Sai kuma ga dattin dake kampe. Ya saka ni ji kamar wani yayi mun amfani da kamfe na.

Na yanke shawara na tambaye yan uwa na ko sunyi mun amfani da kampe na. Suka kalle ni da wani ido suka ce ba wanda zai saka mun kampe na. Suna son su san dalilin daya sa nake tambaya, amma ina tsoron gaya musu. Na san cewa zasu mun dariya.

Ina bukatan sanin abun dake faruwa. Wannan ya saka ni fara aikata wasu irin halayye. Yar uwa ta dake da aure ta lura da halayye na. Ta tambaye ni me ke faruwa. Amma ban san yadda zan gaya mata ba.

Na gaya mata cewa wani jan tawada ne yayi mun datti da kampe na. Tayi dariya kafan ta gaya mun cewa al’ada na ne.

Ta bani audugan al’ada. Ta nuna mun yadda zanyi amfani dashi. Bayan nan ta zaunar dani tayi mun bayanin wasu abubuwa. Ta ce zan iya daukan ciki yanzu. Ta gaya mun na lura da kaina. Tace nayi wanka so biyu a rana idan ina al’ada na. Kuma tace ya kamata na canza audugan al’ada na bayan sa’o’i hudu zuwa shida.

Tace zai dauki dan lokaci kafan na saba da wannan sabon yankin daga rayuwa. Amma duk da haka, tace kada na damu.

Na so na tambaye ta wasu tambayoyi. Amma na dan ji tsoron tambaya. Ina ajiye abubwa sosai a zuciya na.

Nayi wa wasu abokai na magana. Sun amsa wasu tambayoyi na.

Al’adar nan ya rikitar dani. Amma komai ya wuce yanzu. Ko da yake zai yi kyau da ina da wata babba da nake iya yin wa magana kowane lokaci. Ina ganin dai banyi sa’a samun wata kamar haka a kusa dani dana fara al’ada na.

Ba lallai sai kun damu dan baku da kowa kamar Farida idan kuna bukatan yin wa wata magana akan al’adar ku. Zaku iya samun wata da zaku walwala kuyi wa magana, kamar Innar ku, ko kuwa babban yar uwar ku.

Kuna da wata da zaku yi wa magana akan abubuwa kamar al’ada? Kuyi mana magana a wajan sharhi

Share your feedback