Yin magana da uwaye akan matsalolin matasa

Baya zuwa da sauki, amma zaku iya yi

Shekaru na goma sha hudu dana fara al’ada na. Kuma a ranar daya faru, ina tsayiwa a gaban gidan mu dana lura wani abu na gangaro mun a kafa. “Wayo al’ada na “ na fada a zuciya na.

Na san ko menene. An koya mun akan sa a makarantar boko da Islamiya.

“Yakamata na gaya wa mahaifiyata”. Nayi tunani.

Amma akwai dan matsala, ban san yadda zan gaya mata ba.

Kuma ba wai bamu shiri bane. Ina dai kunya yin mata magana akan al’ada ne.

Saboda haka, sai nayi shiru. Har na tabbata cewa na cigaba da yin Sallah ko da yake bai kamata yan mata suyi Sallah idan suna al’ada ba a addinin musulunci.

Nayi tunanin hanyoyi dabam da zan iya gaya wa mahaifiyata. Amma ina ta tsoro.

A karshe, na yanke shawara na gaya mata bayan maghrib. Da maghrib ya zao, na kasa gaya mata.

Na yanke shawara na boye a bayan gida. Na zauna a wajan na minti ishirin. Ba wai ina yin wani abu bane, kawai zama nake.

“Ba zan iya zama a nan kawai ba, yakamata nayi wani abu” na gaya wa kai na.

Sai na kira babban ‘yar uwa ta. na nuna mata dattin dake riga na. Na nuna jahilci duk da yake na san ko menene.

Na gaya mata jinin ya fito daga jiki na ne. Nan take ta kama hannaye na ta jawo ni zuwa falo tana ihu “Mama kizo ki gani, Azeezat ta fara haila”.

Mamman mu ta zo a guje. Yar uwata ta nuna mata dattin a kan kaya na. Naji kunya sosai. Mamman mu ta lura sai abun ya bata dariya.

Sai Mahaifiyar mu ta zaunar dani tayi mun bayanin abun dake faruwa. Ta koya mun akan kawanyar haila. Sai ta nuna mun yadda zanyi amfani da audugan al’ada.

Har tayi mun magana akan yadda zan lura da kai na a lokacin al’ada. Sai ta bani shawara na kiyaye da samari. Ko da yake na san yawancin abun da take magana akai. Amma, na koya sabobin abubuwa.

Na so da bana kunyar yin magana da mahaifiyata ko kowa akan abubuwa kamar al’ada da yin girma.

Hailan ku al’ada ce kuma kada kuji tsoron yin magana da wata amintacciyar yar dangin ku akan sa. Yana da kyau ayi magana. Zaku iya koyan abu daya ko biyu idan kuka yi.

Kun taba samun kanku a al’amarin Azeezat? Dan Allah ku gaya mana yadda kuka bi dashi a sashin sharhi.

Share your feedback