Kungiyar labari

Abokan arziki har abada

Zama abokai tare da Glory da Chioma na daya daga cikin shawara mafi kyua dana dauka wa rayuwa ta.

Sune abokan arzikin nan da kowa zai so ya samu. Kowane minti da su na da nishadantarwa.

Ana maganar “abokai dake zama yan uwa”.

Suna da goyon baya. Su ne abun da za’a kira “kashin baya”

Sun goya mun baya a cikin farin ciki da kuma bakin ciki. Kamar yadda suka tsaya mun sanda saurayi na ya rabu da ni. Domin goyon bayan su, na samu daman share hawaye na bayan al’amarin.

Abu daya mai kyau akan abokantakar mu shine yadda muke yin shagalin juna. Na tuna sanda na fara koyan dinki, su nake amfani nayi tallan kaya na. Kuma dana kare horo na suka taimake ni gaya wa sauran yan mata a al’ummar mu cewa babu wani tela iri na. Domin su, na samu abokan ciniki sosai.

Basu boye mun komai. Bana wayincewa domin su so ni. Kuma idan nayi kuskure, basu hukunta ni ko kuwa suyi mun dariya.

Wannan abokantakar ya koya mun abubuwa da yawa. Na koya akan samari, kudi, rayuwa, har da kidi da waka daga labaran mu. Kuma wasu ranaku idan bamu da amsa wa wasu tambayoyi, Glory na samun amsar daga mahaifiyarta sai ta rarraba da mu.

Wadannan yan matan sun saka rayuwa na yayi sauki koda wasu ranaku muna samun namu bambanci. Amma duk al’amurrar rayuwa na.

Abokai na sun yi a kowane rana a kowane lokaci. Shiyasa nake ba wa yan mata shawara su samu abokai kamar nawa. Ku nema yan mata dake sha’awar abubuwa daya da ku. Kamar yadda abokai na da ni muna son kidi da waka.

Ku samu abokai da zasu taimake ku inganta rayuwar ku.

Kuna bukatan samun abokai dake shekaru daya daku, saboda akwai lokuta da mai yiwuwa kuna son kuyi magana da mutane dake tsaran ku. Amma wannan baya nufin cewa baza mu iya yin magana da mutane dake da masaniya fiye da mu da kuma zasu iya taimakon mu.

Domin ku koya yadda zaku samu abokan arziki ku karanta wannan makalar.

Kuna da abokai dake kara inganta rayuwar ku? Kuyi mana magana akan su a sashin sharhin.

Share your feedback