Baza Su Iya Hana Ki Ba

Tafiya daga ciyawa zuwa alheri

Sannu Springsters, mun karanta wani labari mai wahayi. Dole mu rarraba daku.

Akan wata yarinya mai sunan Sarah Nwosu, wata yar yarinya ce mai shekaru goma sha hudu da babban muradi.

Mahaifiyar Sarah ta rasu da take aji biyu a makarantar sakandare. Ita da yar uwar ta suka koma zama da mahaifin ta da iyalin shi.

Sarah na yawan son karatu da kuma lura da mutane shiyasa take son ta zama likita. Bada bata lokaci ba ta fara yin fiye da kowa a ajin su.

Mahaifin ta nata alfahari da ita. Amma akwai matsala, matan mahaifinta ta bata son Sarah ta samu karin lura fiye da nata yaran. Sai ta kara wa Sarah aikin gida. Tana son Sarah ta kasance da aiki mai yawa saboda kada ta samu lokacin karatun jarabawa. Amma Sarah zata yi karatu kowane dare kuma ta cigaba da cin jarabawa.

Sai matan mahaifinta ta cigaba da cin zarafin Sarah. Ta daina bata kudin motar zuwa makaranta. Sarah zata yi tafiyar fiye da sa’a daya a yawancin ranaku.

Domin ta samu karin kudi, Sarah zata yi wa makwaftar su da yan dangin su aikace aikace a gida.

Amma ta cigaba da karatu sosai. Bata son komai ya hana ta zama likita. Sarah ta samu ta zama daya daga cikin wanda suka ci jarabawan WAEC da JAMB na shigar jami’a a makarantar su.

Amma abun tausayi, mahaifin Sarah ya rasu a wannan shekaran kuma babu kudin da za’a tura ta jami’a.

Amma duk da haka, Sarah bata fida rai ba. Ta koya dinki daga wajan makwaftar su dake dinki. Ta fara samu kudin daga yin nata dinkin. Kuma ta zama mai koyar da dinki wa wasu yara a ungwar su.

Bayan shekara daya, ta ajiye kudi da zai ishe ta shigar jami’a ta karanta darasin da zai sata zama likita. Sarah ta cigaba da dinkin ta da koyar da yaran ungwar su da kuma karatun ta a jami’a. Amma tana tuna cewa makaranta ta ne abun daya fi muhimmanci a rayuwar ta. Tana kaunar kowane aji. Dukka malamai ta sun san ta da tambayoyi masu ingancin.

Da zaran ta kammala karatun ta na jami’a, Sarah ta fara aikin likta a wani babban asibiti a Lagos. Babban muradin ta ya faru.

Labarin Sarah abun mamaki ne ko? Zamu iya koya abubuwa da yawa daga wajan ta. Mu cigaba da kara aiki sosai kuma muyi imani da kanmu, koda rayuwa nada wuya.

Wanda matsaloli ne kika kawar da a rayuwar ki? Ki gaya mana labarin ki domin yayi wahayi zuwa gare sauran yan Springsters.

Share your feedback