Abubuwa da nake son yi da mahaifina

Yadda ni da mahaifina ke kwashe lokaci

Wa zai taba tunanin cewa zan taba shakuwa da mahaifina?

Ban hango sa ba har sai hutun daya wuce da nake gida dashi na mako daya.

Ban taba zama ni daya dashi ba kuma saboda haka ban tabbata yadda wannan zai kasance ba. Na san cewa ba zan iya labari dashi ba. Ko akwai wata a nan dake labari da mahaifinta?

Amma abun ya bani mamaki da komai ya kasance da kyau. Ya aka yi haka, ko?

Ina zama a daki wata rana da mahaifina ya dawo daga aiki. Ya bani wani leda da suya a ciki. Yace ya siyo mun ne. Wannan bai taba faruwa ba.

Sai kuma, ya zauna kusa dani yayi kallon talabijjan. Ya canza shi zuwa tashar wasanni domin ya kalla wani wasan kwallon kafa.

Dana zauna a wajan shiru ina cin suya na, na fara burin sanin dalilin daya sa yake son wasan kwallon kafa sosai, sai na tambaye shi.

Da kun ga yadda fuskan sa ya dau murmushi bayan dana tambaye shi. Ya fara mun bayanin burin sa na zama mai buga kwallon kafa da yake saurayi. Sai ya mun bayani akan masu buga wasan. Ya nuna mun yadda suke wasan.

Koda yake, ban gane yawancin abubuwan da yake fadi ba, naji dadin ganin mahaifina yana labari dani kamar mu tsara ne.

A rana mai zuwa, daya dawo daga wajan aikin sa, ya zo gida da wasu faifan wasan kwallon kafa da yake son mu kalla tare. Kuma ya kara kawo mana suya.

A haka mahaifina dani muka zama abokan kallon wasan kwallo. Kamar wannan shakuwar ya bude mana wawu hanyoyi.

Kafan na sani, ya fara tambaya na abubuwan da nake son yi sosai. Na gaya masa rawa. Yace na nuna masa yadda ake yin sa. Sai ya nuna mun wasu irin rawa na tsofofi da suke yi da suke samari. Abun ya bani dariya.

Nayi farin cikin cewa na kwashe lokaci dashi a wannan makon. Na kara sanin shi.

Domin wannan masaniyar mahaifina dani mun kara shakuwa. Yanzu ina sakewa dashi sosai. Wasu lokuta ina tambayen shi akan samari da kuma rayuwa.

Zan bawa yan mata shawara su jawo kusa da ubanninsu. Suna da nishadi. Ku nema wani abu da suke so sai ku duba kuga ko zaku bunkasa sha’awa a cikin sa. A ta nan zaku iya shakuwa.

Waye a cikin iyalin ku kuka fi shakuwa da? Wani abun nishadi kuka yi dasu? Ku rarraba damu a sashin sharhi.

Share your feedback