Kina tunanin baki da kowa da zaki iya magana da?

Akwai baligin mutane da zaki iya yarda da.

Suna na Sade. Shekaru na goma sha uku. Iyaye na na zama a wani gari da ake kira Osun state. Basu iya duba ni da yan uwa na maza guda hudu ba. Shiyasa nazo ina zama da yar uwar mahaifi na a Lagos. Ina wannan garin tun watar Yuni na shekarar daya wuce. Dana fara zuwa Lagos ina zaman damuwa saboda ni kadai ce.

Yar uwar mahaifi na da kawu na nada manyan yara maza guda uku. Yar uwar mahaifi na na tafiya sosai saboda sana’ar ta. Saboda haka banyi kusa da ita ba. Naji kamar banda kowa da zanyi magana da. Lokacin dana fara al’ada na a watar daya wuce, ban san wanda zan gaya wa ba.

Sai na hadu da wata da ake kira Rita! Tazo makarantar mu a sharadin daya wuce sai ta zama abokiyar zama na. Ina ta murna. Tana da hankali kuma tana da ilmi. Ina gaya mata komai. Harda lokacin da nake da damuwa da maza a makaranta.

Tunda shekarun mu daya ne, bata iya taimako na a kowane lokaci ba. Tace ina bukatan wani baligin mutum da zan iya yin wa magana. Tace nayi magana da Yar Uwar mahaifi na. Tace kawai saboda Yar uwar mahaifi na tana yawan tafiya ba zai hana mu kusa da juna ba. Ina ta jin tsoro, amma na gaya wa yar uwar mahaifi na akan al’ada na a mako daya wuce. Ta taimake ni sosai! Ta gaya mun akan abubuwan dake faruwa da jiki na. Harda wasu abubuwa da Rita bata san komai akai ba!

Rita ta nuna mun cewa ba sai naji tsoron yin magana ba. Koda yar uwar mahaifi na bata kusa, zan iya yin wa mai bada shawara a makarnatar mu magana. Na samu mutane da zan iya yarda da. Harda babban dan yar na mai suna Mark. Wasu lokuta, ina zuwa wajan sa domin shawara akan maza.

Yanzu na san cewa bai kamata nayi shiru idan naji kamar abu ba dai dai bane. Idan ina da matsala ko kuwa ina jin tsoro akwai mutane da zasu taimake ni.

Waye ne baligin mutumin nan da kika yarda da? Gaya mana akan abubuwan da kike musu magana akai a shafin sharhin mu.

Share your feedback