Wannan yaron ya cigaba da damu na

Yadda mahaifiyata ta taimake ni

Tunanin ku (3)

Shekaru na goma da wani tsohon yaro ya fara gabatowa waje na. Na tuna da ranar sarai. Ina shagon iyaye na yadda na saba a gaban gidan mu. Mahaifiyata taje kasuwa kuma yan uwa na sun je makaranta. Mahaifina ma kuma baya gida.

Wani tsohon yaro dake zama kusa da gidan mu yazo siyan wani abu. Na lura cewa yana kallo na da wani irin ido. Nayi kokarin kauce idannun sa. Na tambaye shi abun da yake so ya siya. Yake ta gabato kusa dani da nake daukan abubuwan da yazo siyowa. Wannan ya hana ni walwala.

Na lura bayan ranar ya fara zuwa shagon koda yaushe. Wasu lokuta zai gwada saka ni fitowa daga shagon na same shi. Har ya tambaye ni ko zan iya haduwa dashi a bayan shago yadda ba wanda zai gan mu. Na tabbata nace a’a duk sanda ya tambaye ni na hadu dashi a bayan shago. Wannan saboda na san cewa haduwa dashi ni kade zai iya jawo hatsari.

Duk da yadda nake tace masa a’a yaki fid da rai. Ya cigaba da gwada saka ni haduwa dashi.

Na san cewa dole nayi wani abu domin na saka shi ya daina. Sai wata rana da nake magana da mahaifiyata na lura cewa tana cikin farin ciki. Nayi tunani cewa lokacin nan ya dace na kai rahoton wannan yaron a wajan mahaifiyata. Sai da muka yi shiru nace mata “Mama akwai yaron dake yawan zuwa shago ya dame ni, na gaya masa ya daina zuwa amma yaki ji. Yana yawan gaya mun na hadu dashi a bayan shago amma naki masa shi!”

Mahaifiyata ta tambaye ni ko wanene sai na gaya mata akan sa.

Mahaifiyata taje gidan sa ta kai rahoton sa a wajan matan mahaifinsa. Ta bashi kashedi sosai. Tun daga ranar ya daina damu na.

Yanzu hankali na ya kwanta da ya daina damu na. Kuma nayi alfahari da kaina dana kai rahoton sa a wajan wani daya girme ni.

Shekaru sun wuce tun da abun nan ya faru. Wasu lokuta idan na gan sa sai na tuna yadda ya saka ni jin wani iri da yadda ta gabato ni. Har nayi tunanin abun da zai iya faruwa da ban cigaba da jin tsoron kai rahoton sa ba.

Domin matakin dana dauka yanzu na san yadda zan fuskance sauran samari a ungwan mu dake damu na da kuma tambayana na fita dasu.

Wa masu taurin kai ina kai rahoton su a wajan iyaye na.

Bana tsoron kai rahoton kowa ko kuwa yin musu magana. Kuma zaku iya yin haka.

Share your feedback

Tunanin ku

Godiya

March 20, 2022, 7:58 p.m.

YAYI

March 20, 2022, 7:58 p.m.

Tinanikowa

March 20, 2022, 7:57 p.m.