Wannan yaron na fadin miyagun abubuwa

Yadda na bi da jita-jita

Ina aji daya a jami’a da nayi masaniyar nawa rikicin samari na farko.

Wannan yaron da nake magana akai aboki na ne Jide.

Yana nan kamar dan uwa na a makaranta. Yana taimako na da al’amurar makaranta koda yaushe.

A lokacin karatun jami’a na biyu, na lura cewa halayar sa na canzawa. Ya fara guje na. Baya cika mun magana.

Nayi masa magana wasu lokuta akan ayyukan sa. Amma duk da haka halayar sa basu canza ba.

Bayan lokaci kadan, ya daina mun magana gaba daya.

Na zata baya so na a kusa dashi ne kuma. Sai na yanke shawara na share shi.

Komai na tafiya daidai har sai lokacin da wata yarinya ta same ni wata rana. Ta gabatar da kanta a matsayin budurwar Jide.

Nayi mamakin cewa Jide nada budurwa.

Tace ta so mu hadu ne kawai. Muka musayar lambar waya sai ta tafi.

Bayan sati biyu, Jide ya same ni. Ya gaya mun na nisanta kai na da buduwar sa. Yayi kamar yana kare ni ne.

Abun mamaki bayan maganar mu sai yaje yana gaya wa mutane wai ina son sa. Yace ni na saka buduwar sa ta rabu dashi. Har yana zagi na.

Ban san abun yi ba. Abun ya bata mun rai kuma ya saka ni bakin ciki.

Na kasa tafiya ni kadai a makaranta.

Ina bukatan wani da zan iya yin wa magana. Nayi wa mahaifiyata magana. Duk da yake ban gaya mata cewa Jide bane ne. Mahaifiyata tace;

Baza ki iya iko da abun da mutane ke fadi ko kuwa suke tunani akan ki ba. Duk da haka, kada ki taba bari wannan ya canza ki.

A rayuwa, wasu mutane zasu iya yin miki abun alheri kuma wasu zasu yi dabam. Saboda haka, kada ki bari wannan masaniyar ya saka ki ji kamar kowa na nan haka ne.

Naji dadi da kika mun magana. Amma ina son ki kai rahoto a wajan hukumar makarantar ku. Ya kamata ya baki hakuri. Yana bata miki suna kuma wannan bai dace ba.

Kafan nan, kiyi kokari kada ki dame kanki da wannan matsalar. A lokaci kadan, mutane zasu manta da wannan labarin. Ki maida hankali kawai da makarantar ki.


Mahaifiyata ta fadi gaskiya. Bayan lokaci kadan, mutane suka daina magana akan sa.

Ina son na gaya muku cewa idan kuka same kanku a irin wannan al’amarin kuyi magana. Ku kai rahoton mutumin a wajan wani babban mutum ko kuwa a wajan hukuma. Zaku iya yin wa iyayen ku magana, ko Innar ku ko kuwa wani mallami. Zasu iya baku shawara akan abun yi.

Kun taba samun kanku a irin wannan al’amarin? Ku gaya mana yadda kuka bi dashi a sashin sharhi.

Share your feedback