Ba lallai bane yan mata da maza suyi soyayya
Da farko banda lokaci wa Stanley. Baya magana sosai. Mutane sunce yana da dagin kai.
Amma sai muka fara magana a gidan abokiya ta. Stanley da dan uwan sa na zama damu a daki. Suna labari akan wani takarda mai nishadantarwa. Da kun ga fuskan su da nace na taba karantawa. Basu san kowane yarinya da take son karanta irin takardar nan ba. Na burge Stanley. Kai na sai kara kato yake tayi.
Da ni da Stanley muka fara musayar takardun nishadantarwa. Muna son irin haruffa daya. Muna dariyar abubuwa iri daya. Muna son abubuwa iri daya. Baya son yaji a abinci. kamar ni. Yana tsoron karnuka, Kamar ni. A lokaci kadan, na lura cewa bai da dagin kai. Yana da kunya ne kawai.
Muka fara yin amana da juna. Ni na fara sanin cewa yana son ya zama mai fenti. Ya nuna mun zane-zanen sa. Suna da kyau sosai. Na gaya masa cewa ina son na koya wasan tanis. Wannan yammar, ya fara koya mun a cibiyar al’ummar mu. Da abokan mu suka gan mu, suka fara tsokanan mu. Suna kiran mu mata da miji. Suna kiran Stanley “mai son mata”.
Naji kunya. Naji kamar ina yin abun da bai kamata ba. Amma Stanley yayi dariya yace, “Mu abokai ne kawai”
Gaskiya, ban tsamani ina son mu cigaba da abokantakar kuma ba. Bana son mutane na gulma na. Amma kuma bana son nayi asarar sa. Na rikice kuma ina bakin cikin.
A gida, na bude ciki na wa yar uwar mahaifiyata. Ta gaya mun kada na damu da abun da mutane ke fadi. Tace Stanley nada hankali, saboda haka kada na kashe abokantakan mu. Wannan ya saka hankali na ya kwanta.
Yanzu Stanley ya zama babban abokina. Muna gaya wa juna komai. Muna taimakon juna idan muna bukata. Koda bamu tare, muna cigaba da magana. Ya zama dan uwan nan da ban da.
Labarin Mimi misali ne mai kyau mai nuna cewa yan mata da maza zasu iya zama abokai. Akwai abubuwa fiye da yin soyayya a rayuwa.
Kina da babban aboki namiji? Gaya mana labarin ki a nan kasa.
Share your feedback