Menene wannan jan dattin?

Sannu al’ada

A makonni kadan bayan ranar haihuwar ta na goma sha uku, Alice ta lura da wani datti a rigar ta. Tana zama a gida kawai ba zato ba tsammani ya zo! Ta kasa gane daga inda yazo. Ta duba jikin ta. Sai taga cewa jinin na fitowa daga farjin ta ne!

Alice ta fara gigitawa.

Har ta fara kuka sanda mahaifiyarta ta shigo gida

. “Mama, akwai wani abu dake damu na. Ina zub da jini. A can kasa! Zan mutu ne?” Alice ta fara zubar da hawaye. Ta nuna wa mahaifiyarta jinin.

Mahaifiyarta ta rungume ta kuma ta kwantar mata da hankali.

“Yar ta, ba mutuwa kike yi ba kuma ba ciwo kike yi ba. Kin fara al’adar ki ne kawai. Kin san ko menene wannan?

Alice taji yan mata a makaranta suna magana akan sa, amma bata tabbata ma’anar sa ba. Mahaifiyarta tayi mata bayani.

“Idan jikin yarinya ya fara balaga, wani abu da ake kira al’ada ko jinin haila na farawa. Yawancin mutane na kiran sa ganin al’ada. Wannan yana nufin cewa so daya a wata, zaki zubar da jini daga farjin ki.”

Wannan ya kara saka Alice fargaba, “Ban shirya haifan yaro ba! Ina aji biyu ne kawai a makaranta!”

Mahaifiyarta tayi dariya, “A’a mana yar ta, ina nufin cewa jikin ki ya shirya. Yana nufin cewa yanzu, zaki iya daukan ciki. Ba wai cewa ki yi ba yanzu.”

Hankalin Alice ya dan kwanta, amma har yanzu ta rikice. ”Me ya shafe daukan ciki da zubar da jini so daya a wata?”

“A cikin jikin ki”, Mahaifiyar Alice ta saka hannu a kan cikin ta, “Kina da wani abu da ake kira mahaifa. A wajan jarirai ke girma. Kuma kina da wajan da ake samar da kwai, a nan ne jikin ki ke ajiyar kwai. Kowane wata, ma’ajiyar kwan ki na sake kwai. Zai yi tafiya cikin mahaifan ki. Idan mace tayi jima’i, wasu lokuta wannan kwan zai nuna idan ya hadu da maniyin namiji. Wannan kwan ne zai zama jariri. Yanzu, idan ma’ajiyar kwan ki zai sake kwai, rufin nan a cikin mahaifar ki zai kara kauri idan jariri na bukatan yin girma. Idan kwan bai nuna ba, toh jikin ki zai zubar da wannan rufin. Saboda haka, idan al’adar ki ya zo, toh wannan rufin ne ke fitowa.”

Alice tayi tunanin wannan. “Wannan yana nufi cewa kowane wata jiki na na shirin daukan ciki? Kuma idan bai faru ba, zan ga al’ada na?”

Mahaifiyarta tayi murmushi tace “Eh. Kin ga, dukka wannan abun al’ada ne. Kada kiji tsoro.”

Sai mahaifiyarta ta nuna mata yadda zata yi amfani da audugan al’ada kuma tayi mata bayanin yadda zata tsaftata kanta a lokacin al’adar ta.

Alice tayi sa’ar samun wata kamar mahaifiyarta da zata yi magana da. Idan kuna son karin bayanai akan al’ada, ku duba nan

Wa kuka sama a lokacin al’adar ku na farko? Ku gaya mana akan sa a sashin sharhi. Ko baku fara al’adar ku ba? Kar ku damu, dukkan mu na musamman ne kuma jikin mu na bunkasa a lokuta daban.

Share your feedback