Idan abokai suka yi fada

Koya cewa ba komai bane idan kuka banbanta da sauran mutane

Abokantaka na da Adaobi ya fara tun da muke shekaru shida. Tun ranar da iyalin ta suka dawo mahadin mu, mun shaku sosai. Muna zuwa ko ina tare. Mutane na kiran mu yan biyu. A gaskiya, nayi kusa da ita fiye da yar uwata. Sai wata rana, muka yi fada.

Akwai wani abu daya akan Adaobi dake bani haushi. Akwai ta da iya bata lokaci. Tana sa mu yin makaran kowane abu. Musamman ajin gwajin rawa da muke zuwa. Kuma na tsana yin makaran wannan ajin.

Nayi mata maganan sau da yawa. Amma bata saurara ba. Sai makonni kadan da suka wuce, muka kara makara kuma. Wannan lokacin, mun shiga matsala da mai koyar damu. Mallamin yayi mana ihu kuma ya bamu horo. Abun ya bata mun rai sosai.

Nayi mata ihu sosai. Nake ta tambayen ta dalilin daya sa take son bata lokaci. Sai tayi haushi. Tace na daina gwada canzata. Tace dani abokiyar kwarai ne, zan karbe ta a yarda take. Na kasa yarda cewa baza ta bani hakuri ba bayan laifin ta ne aka bamu horo. A ranar muka daina magana.

Bayan kwanaki kadan, mahaifiyata ta lura cewa Adaobi bata zo gidan mu ba. Ta tambaye ni akan sa sai na shafa mata labarin. Sai ta bani wani shawara mai ban sha’awa:

“Bai kamata kiyi wurgi da abokantaka domin kinyi fada da wani. Musamman bayan kun dade da abokantakar. Ke da Adaobi daban ne. Kina da naki halayye, baku ayuka iri daya. Wasu lokuta zai jawo matsaloli. Amma al’ada ne. Kuma babu matsala. Kawai dai zaki bi dashi da wayo ne ba tare da yaranta ba. Bai kamata kuyi wa juna ihu ba. Koda kuna haushi sosai. Ku dakata sai hankalin ku ya kwanta, sai ku zauna kuyi magana. Girmama juna nada muhimmanci sosai a abokantaka. Idan kuka yi magana, ki tambaye ta abun dake dauka mata lokaci. Aikin gida ne? Ki ga ko zaki iya taimakon ta. Zata miki godiya. Ko kuwa ki gwada zuwa gidan su da sauri kafan lokacin ajin ku. A ta nan zaki iya saka ta yin shiri da sauri. Kuma zaki iya yin mata bayanin dalilin daya sa tafiya ajin da sauri ke da muhimmimanci a wajan ki. Mai yiwuwa bata yi tunanin sa ba kamar yadda kike yi ba. Yafi ki gwada samun hanyar taimako a maimakon yin fada da ita ta.”

Na gwada abun da mahaifiyata tace. Na lura cewa ya taimake Adaobi gyara halin ta na makara. Saboda shawarar mahaifiyata, na koya yadda zan tafiyad da abubuwan da suka banbanta mu.

Domin ku kara samun bayanai akan gina abokantaka masu kyau ku duba nan

Kuna samun sabani da abokan ku? Ku gaya mana yadda kuke shawo kan matsalar a sashin sharhin mu.

Share your feedback