Ku tsaya da karfi, kada ku fid da rai
Da nake shekaru bakwai, wani abu mara kyau ya faru. Wani dan dangin mu ya taba ni a yadda bai dace ba- a wani hanya daya hana ni sakewa.
A ranar daya faru, naje dakin sa nayi kallon wasan kwaikwayo kamar yadda na saba yi wasu lokuta.
Ban taba tunanin ko zai iya mun lahani ba.
Nayi mamaki bayan daya faru. Nayi bakin ciki sosai. *Meyasa wannan abun da faru dani? Me nayi da daidai ba? Na tambaye kaina.
Meyasa ba wanda ya ceci ni? Wannan ya saka ni jin rashin tsira ko ina cikin mutane. Na kasa yarda da kowa kuma.
Al’amarin ya saka ni fara kin jinin mahaifiyata. Naji kamar ta karya mun zuciya. Mai yiwuwa da tana zaman gida sosai, da ta hana abu kamar haka faruwa.
Na bata laifin komai. Amma sai na lura cewa bata da wani ra’ayi. Ita guda ke aiki domin ta lura da yara hudu. Saboda haka, sai na fara bawa mahafina marigayi laifi. Me yasa ya mutu? Meyasa ya bar mahaifiyata tayi komai da kanta?
Nayi bakin cikin sosai. Na kasa yin wa kowa magana akan sa. Ina tsoro zasu bani laifi. Su mun dariya. Su kira ni mara tarbiya.
Sai nayi shiru.
So daya ko biyu na yanke kaina da reza. Ina tunanin mai yiwuwa idan na ji wa kai na ciwo zan dan ji dadi.
Sai kuma, akwai wasu ranaku da nake ji kamar na kashe kai na. Ina bakin ciki sosai.
Takardar sirri na ya zama abokina.
Dana yi girma, na kasa yin hurda da samari. Na kasa yarda dasu. Na tsane su duka.
Da shekaru suka wuce, ajiye wannan sirri yayi mun wuya. Sai wata rana, na fashe da kuka. Na kasa boye sirrin kuma. Na gaya wa mahaifiyata da yar uwata.
Mamman mu tayi fushi sosai. Ta kasa yarda. Ya za’a yi na boye mata abu kamar haka? Tayi bakin ciki.
Tayi kuka ta rungume ni bayan nan. Ta saka ni nayi mata alkawarin cewa bazan kara boye mata komai ba kuma. Tace kada naji tsoron kawo rahoton kowa a wajan ta.
Tayi alkawari cewa zata goya mun baya.
Ko da yake, shekaru da yawa sun wuce da abun ya faru. Kuma, ina farin ciki yanzu fiye da da. Bana tunanin yanke kaina ko kuwa kashe kaina kuma. Ina kan aikin daina kin jinin maza.
Kuma, har zanzu ina kasa yarda da maza. Amma, ina farin ciki dana rarraba sirri na. Kuma ina fatan wannan zai karfafa sauran yan Springster suyi magana akan kowane abu mai lahani daya faru dasu.
Sannu Springster, kuna cancanin girmamawa koda shekarun ku nawa ne. Idan wani ya hana ku sakewa, ku gaya musu kuma ku kai rahoton su zuwa wajan wani amintaccen babban mutum kamar iyayen ku ko kuwa mai tsaran lafiyar ku.
Idan kuna nan kamar wannan yarinya a labarin mu na yau kuma kuna bukatan taimako, dan Allah ku kira Cece Yara a wannan lambar 08008008001. Su ke kula da layin taimakon a kyauta, kuma suna nan a shirye suyi magana daku akan kowane abu dake damu ku game da al’ada, samari ko kuwa balaga.
Lambobin su na nan a bude Litinin zuwa Jumma’a daga karfe tara na safe zuwa karfe biyar na yamma. Masu lambobin Airtel na iya kira a kyauta.
Maganar ku dasu na amana ne saboda haka ba sai kun bada sunnan ku da bayanin ku ba. Zaku iya yin tambayoyi kuma ku samu goyon baya da kuke bukata.
Share your feedback