Zai iya wuya ki zabe daga abun da kike so da abunda iyayen ki ke so
Iyayen mu. Muna basu girma. Munyi girma a karkashin rufin su. Sun bamu duka abunda muke dashi. Muna da yanki dasu. Muna son mu sa su jin alfahari da mu da kuma farin ciki. Amma, muma muna da burin mu. Muna da namu kai da zaciya.
Da Azeezat ke karamar yarinya, mahaifin ta yaso ta zama likita. Amma Azeezat taso ta zama marubuci. Bata taba raba wannan burin ta da iyayen ta ba. Zata kwashe lokaci da dare saboda ta karata takadu da kuma rubutu.Sai ta kwashe lokaci a ranakun ta tana karatu ta zama likita.
Yanzu da ta zama likita, Azeezat na fadi cewa “ ina da na sani da ban gaya wa iyaye na akan buri na ba. Bana son sauran yan mata kamar ni suyi irin kuskuren nan. Dana gaya wa iyaye na."
"Wa ya sani, kilan da sun goya mun baya sun taimake ni karatu na zama marubuci ko ma su yarda na je wajan ma’aikatar masu rubutu. Yanzu bazan sani ba dan ban taba gaya musu akan abun da nake son nayi ba."
"Mai yiwuwa da na kara kokari na ja kusa da iyaye na ina musu magana akan buri na kuma ina kwashe lokaci dasu da sun taimake ki. Kowane yarinya na bukatar sanin cewa magana na taimakon shawo kan matsala.”
Ki gaya wa iyayen ki akan burin ki. kada ki tunanin cewa baza su ji ki ba. Suna son cin gaban ki. Wannan yana nufin cewa suna son ki samu farin ciki, idan kika musu magana da gaskiya, zasu ga cewa burin ki nada muhimmanci.
Kin gaya wa iyayen ki akan burin ki?
Baki son ki kara rayuwar ki kina tunanin "Da ace na musu magana fa?”
Idan baki yi tunani da kyau akan shi ba toh muna baki shawara
Yana da muhimmanci kiyi wa iyayen ki magana akan abun da kike so. Yana da muhimmanci kuma ki saurara abun da suke tunani. Tare, zaku iya yanke shawara mai kyau.
Share your feedback