Hanyar wa ya kamata ku bi?

Rayuwar ku, ra’ayin ku.

Babu abu mafi wuya kamar zabi tsakanin abun da kuke so da kuma abun da iyayen ku ke son muku.

Halin dana same kai na kenan a shekaru kadan da suka wuce.

Na so na zama yar wasan kwallon kafa amma iyaye na na son na zama likita. Sunce kasancewa likita zai saka mutane su kara girmama ni kuma ya kawo mun kudi sosai. Kuma suka ce wasan kwallon kafa ba aikin yan mata bane.

Domin haka ne na saurare su. Kuma bana son na nuna rashin biyayya. Na shirya yin abun da zai saka iyaye na yin alfahari dani.

A haka na same kai na a jami’a ina karanta darasin zama likita. Amma da lokaci ya dan wuce, na fara damuwa cewa bana cimma burina. Ya dame ni dana watsi da burina.

Idan na kalla baya yanzu, ina ji dama nayi kokari na bayyana wa iyaye na. Mai yiwuwa dana gaya musu yadda nake ji zasu yarda na cimma burina na zama yar wasan kwallon kafa.

Eh, iyaye na nan domin su jagorar damu, amma muma muna da matsayi mai muhimmanci a yanke shawara da zai shafe rayuwar mu.

Na san wasu lokuta yin magana bai zuwa da sauki, amma yana yiwuwa.

Saboda haka, shawara na wa kowane mutum dake cikin irin wannan al’amarin shine ku bi burin ku. Kuyi iya kokarin ku kuyi wa iyayen ku magana ko kuwa wadanda ke tsaran lafiyar ku akan muradin mu.

Kada ku bata lokaci kuna tunani akan dukka abubuwan da zaku iya yi da baku yi ba bayan zaku iya gayra shi ta yin magana.

Koda yake ni likita ce yanzu, ina kan buga kwallo da yan karamin kungiyar na kuma ina tunanin zama mai wasan kwallo a nan gaba.

Wasu ranaku, ina gayatar iyaye na su zo su kalla wasani na.

Duk da yake, basu tabbata da wannan burina ba amma duk da haka sun shirya goyon baya na.

Kada ku matsa wa kanku ku akan zaben buri na kwarai. Rayuwa tafiya ne ba gudu ba. Saboda haka koda kun fara tafiya a wani hanya kuma kuka lura cewa ba abun da kuke so bane, zaku iya juya ku canza hanyar ku. Bai yi latti ba ku cimma burin ku.

Wanne hanya ne kuke sha’awa ku dauka? Ku rarraba martanin ku da mu a sashin sharhin ku.

Share your feedback