Safgar ki zai iya zama rayuwar ki na gaba

Idan kina kaunar abun da kike yi, zaki yi murnar aikata shi kuma zai yi sauki.

Hanya daya da zaki samu farin ciki shine ki samu abun da kike son yi sosai a duniya. Sai ki maida shi aikin ki.

Kowa na tunanin Binta ta zama malamar asibiti, ko likita, ko kuwa ma’aikatar gwamnati. Tana da wasu abubuwa da ta tsara zata yi. Abunda take son yi shine gyara kayan lantarki a gida. Ta gaya wa iyalin ta tana son ta zama mai koya aiki a wajan mai gyaran kayan lantarki. Sun yi mamaki kuma sun yi bakin ciki. Binta ta nace har sai da ta shawo kan iyalin ta. Yanzu ita ce mace na farko a al’ummar su dake aikin gyaran kayan lantarki.

Kasuwanci ta na tafiya da kyau. Tana samun kudi dai dai da zai taimake ta lura da iyalin ta. Tana koyar da wasu yan mata dake son zama masu gyaran kayan lantarki.

Binta tace, “lokacin dana yanke shawara na zama mai gyaran kayan lantarki, ban san ko zan ci nasara ba ko zan fadi. Kawai na san cewa zan yi dana sani idan ban gwada ba. Shine shawarar mai mafifici dana yanke domin yanzu ko wanda rana zan riga yin abun da nake son yi.”

Kina son daukan hoto? kina da kwarewar mai zane zane? Abokai ki da iyalin ki na tambayan ki taimako a wani abu da kika iya sosai? Da kyau, domin mai yiwuwa kin samu aikin ki na nan gaba!

Samun riba a kasuwancin ki mai sauki ne. Baki bukatar kudi sosai ki fara. Zaki iya farawa a gida. Baki bukatar wani ofishi ko wani fili. Ki jibinci abokai ki da iyalin ki a aikin ki.

Kina budurwar ki, Saboda haka kina da sauran lokaci da zaki samu abun nan da kike matsananci. Kada ki damu idan baki tabata ba tukun. Ki amfani da lokatar ki kina binciko abubuwa da zaki iya zabi. Idan kika samu abun da kike so, zaki sani.

Share your feedback