Yadda zaku kara shakuwa da iyalan ku
A shekarar daya wuce Amina ta so iyalin ta su kara shakuwa.
Tayi musu magana akan sa kadan amma babu abun daya canza.
Taso dama iyalin ta su zama kamar na abokiyar ta Titi.
Iyalin Titi sun hadu kuma sun shaku.
Suna yin komai tare. Suna halarta taro tare.
Koda yaushe suna yin wasan ludo tare.
Tana sha’awar iyalin su.
Wata rana Amina ta ziyarta gidan su sai ta gan su suna kallon wani wasan kwaikwayo da ake kira Jenifa. Sun nuna alama kamar suna jin dadin sa sosai.
Wani ra’ayi ya shigo mata kai. Zata rinjayi yan uwan ta suyi wani abu tare.
Tayi tunanin akan saka su zuwa cin abinci tare domin yawancin lokuta suna cin abinci a lokaci dabam.
Da ta kai gida ta tambaya ko zasu iya zuwa cin abinci tare kamar saurar iyalai.
Da farko abun ya bawa yan uwar ta dariya.
Sunyi shakkar zuwa.
Amma ta dage ta gaya musu dalilin.
Bayan lokaci kadan sa suka yarda su gwada zuwa.
A wajan cin abinci ta tabbata ta tamabaye kowa akan ranar sa. Sai ta kokarin basu labari akan sabobin abubuwa dake faruwa.
A dan lokacin kadan suka fara bude baki suna magana da juna.
Yan uwan ta na son lokacin cin abincin dare.
Iyayen su suka lura canjin sai suma suka fare hade dasu wasu lokuta suyi labari.
Lokacin cin abincin daren su ya zama lokacin shakuwar su. Kowa ya fara saka rai wa lokacin.
Lokaci ne da zasu yi magana akan ranar su, su bawa juna shawara kuma su koya abubuwa da yawa daga wajan juna.
Lokacin cin abincin su yayi wa amina da yan uwan ta sauki suyi wa iyayen su magana.
Yayi wa Amina sauki ta walwala ta tambaye iyayen ta tambayoyi akan samari, jikin ta, harda lafiyar ta.
Amina na farin ciki akan yadda ita da yan uwan ta da kuma iyayen ta suka shaku yanzu.
Iyalin ta sun kara shakuwa yanzu fiye da da.
Wasu lokuta kuna marmarin kara shakuwa da yan uwan ku ko iyayen ku? Kuyi wani abu akan sa. Kuyi musu magana akan sa. Ku nemo wani abu da suke son yi sai ku kokarin yin sa tare.
Ku gina dangantaka da su a hankali. Yan uwan ku da iyayen ku zasu iya zama abokan ku.
Share your feedback