Yadda zaku tsaftata kanku da kuma samun lafiyar jiki
Kasancewa da lafiyar jiki na bukatan samun kiwon lafiya mai kyau. Wannan yana nufin lura da kanku domin ku kauce rashin lafiya.
A nan kasa akwai wasu dabi’u da zasu taimake ku samun lafiyar jiki.
Yin wanka koda yaushe
Musamman idan kuna waje a gaba dayan ranar. Wannan zai hana kwayan cututtukka shigan jikin ku. Idan zaku iya,kuyi wanka so biyu a rana (da safe da kuma dare). Idan kuna wanka ku riga wanke hammatan ku. Wannan zai taimaka hana warin dake zuwa da zufa a wannan bangaren.
A lokacin al’adar ku, yana da muhammanci kuyi wanka so biyu a rana. Kuyi kokarin yin wanka da ruwan zafi, zai hutar muku da gabobin jiki musamman idan kuna ciwon ciki.
Kada ku wanke farjin ku da sabulu. Ruwa kawai ya isa.
Ku wanke hakoran ku
Ku wanke hakoran kowane rana. Amma idan zaku iya, ku wanke shi kafan ku je bacci.
Wanke hakora koda yaushe na rage kwayan cututtukar baki. Wanke hakora na taimakon kashe kwayan cututtuka dake jawo ciwon hakori, ko ciwon dasashi, ko kuwa rummuka a hakora. Gaskiyar shine, kwayan cututtuka dake jawo ciwon dasashi na iya kai har zuciyar ku, kuma wannan zai iya jawo matsala. Bamu son wannan ya faru.
Ku wanke hanayyen ku
Kafan ku ci abinci ku wanke hannayen ku. Bayan kunyi amfani da shadda ku wanke hannayen ku. Idan kuka dawo gida bayan kunyi wasa a waje, ku wanke hannayen ku. Wanke hannayen ku koda yaushe zai taimaka hana bazar da kwayan cututtuka da zai iya saka ku ciwon.
Yan mata, kuyi gwajin wadannan dabi’un ku tsirata kanku.
Wandan sauran dabi’un ne kuke yi? Ku rarraba damu a sashin sharhi.
Share your feedback