Sassan jiki guda hudu dake bukatan lura da na musamman

Siddabaru lafiyan jiki

Yawancin mu mun san cewa muna bukatan lura da zuciyar mu, da hanta, da kuma hunhu.

Amma sauran mu fa?

Gaskiyar shine, dukka sashin jikin mu nada musamman kuma ya kamata a lura da shi.

Kina al’ajibin sasin jikin ki dake bukatan lura na musamman? Toh ga wasun su.

KAFAFU
Mai yiwuwa yin lura da kafafun ki bas hi bane abun yin kin a farko. Amma mun tabata cewa babu wanda yake son kafa mai wari.
Zufa ne ke yawan sanadin warin Kafafu. Kuma yin amfani da takalmin daya koda yaushe na jawo doyi.
Yadda zaki kasha warin?
Ki yada takalmin a waje koda yaushe.
Kiyi kokari kada kiyi amfani da rufafen takalmin koda yaushe.
Ki wanke kafafun ki da sabulu ko wanda dare. Kada ki manta ki wanke tsakanin yatsun. Kuma ki tabata kin busar da su sosai.

FARCE
Koda farcen ki ne ko yatsun ki, yana da kyau ki lura da farcen ki.
Ki rage su ko ki yanke su koda yaushe. Ki tsaftace su. Ki tabata baki da datti a karkashin su.
Jika farcen ki a cikin ruwa da dadewa na iya bata su. Ki tabata ki busar da su da kyau bayan kin wanki kwanika ko tufafin ki.
Zaki iya kara masa launi da lalle.

HAMATA
Hamata mai zufa da rashin tsafta zai iya sanadin warin jiki.
Ki wanke hamatan ki da kyau idan kina wanka.
Zaki iya yin amfani da tirare a karkashin hamatan ki saboda ki rage zufa. Suna zuwa kamar feshi ko a kwalba dake da kwallo mai mirgina. Zaki iya siyan su daga kantin siyar da magani.
Gashi a hamatan kin a iya sanadin zufa. Wasu mutane na yanke ko rage gashin hamatan su. Ya rage miki idan kina son kiyi wannan.

SASHEN FARJI
Farjin mu waje ne na musamman kuma marasa karko. Ya kamata mu lura su. Saboda haka ki tabata baki maimata kampai ko kiyi amfani da kampai da wani. Kada ki wanke farjin ki da sabulu. Ruwa yayi.
Ki lura da wajan shaddar da kike amfani saboda ki guje cuta.
Ki tsaftace gashin farjin ki.
Ba kome bane idan farjin ki na fitar da wasu abubuwa masu launin kwai ko madara. Kuma kowane farjin nada nasa wari na dabi’ance. Amma idan kika lura da wani wari ko wani abu na fitowa dake da launin kasa ko kore kiyi Magana da wani babba da kika yarda da ko kije kiga likita tun da wuri.

Ya kike lura da jikin ki? Rarraba mana siddabarun a shafin sharhin mu.

Share your feedback