Ga gaskiyan……...
Mai yiwuwa kinji wasu labarai akan yadda zaki dauka ciki ko kuwa yadda zaki tabata baki dauka ciki ba.
Gaskiya, hanya guda da zaki tabata baki dauki ciki ba shine idan baki yi jima’i ba. Rashin yin jima’i na taimaka tsare ki daga kwashen cuta da ake samuwa ta hanyar jima’i.
Ana samun yara idan maniyyi daga namiji (ko yaro) ya hade da kwayaye daga mace (ko yarinya). Idan ma’aurata suka yi jima’a, maniyyin na yin iyo daga jikin namijin cikin jikin macen.
Mata da yara mata nada wani waje mai musamman a jikin su da ake kira mahaifa. Maniyyin na yin iyo zuwa wajan. Idan akwai kwai a wajan, toh za’a iya hada yaro.
Yanzu da kika san asalin labarin, ga wasu karyan labarai da bai kamata ki yarda ba.
1. Mace baza ta iya daukan ciki ba a ranar da ta fara jima’i
Matukan dai da yarinya ta fara al’ada, zata iya daukan ciki. Ba komai ko da ranar farkon ta ne ko na biyar.
2.. Yarinyan da take al’ada baz
a ta iya daukan ciki ba
Maniyyi na iya zama a cikin jikin mace har zuwa kwana biyar. Idan mace tayi jima’i a karshen al’adan ta, zata iya daukan ciki.
3. Idan mace ta wanke jikin ta nan take bayan jima’i, baza ta dauka ciki ba
Maniyyin na yin iyo a can cikin jikin macen. Babu irin wankin da zaki masa da zai fitar dashi.
4. Idan mace tayi tsalle nan take bayan jima’a, baza ta dauka ciki ba
Da zaran maniyyin ya shiga jikin mace, yin tsalle ba zai fitar dashi ba.
5. Kinyi kankanta ki dauke ciki
Da zaran yar mace ta fara ganin al’adan ta, zata iya daukan ciki. shekarun ta ba komai bane.
Gaskiyar shine, yadda zaki hana aukuwar abun nan shine idan baki yi jima’i ba. Duk da haka, akwai hanyoyi da zaki iya rage daman nan. Idan kina damuwa akan daukan ciki, kiyi wa wani ma’aikacin asibiti magana ko kuwa wani daga cikin iyalai ki. Zasu iya tattauna akan kwayoyin haihuwa da zaki iya amfani.
yanke Shawaran yin jima’i na bukatar tunani a tsanake. Ki guje wanda zai matsa miki lambar akan yin abun da zai saki cewa da na sani anjima.
Idan kin rikice akan wannan abun, kiyi magana da wani babba da kika yarda da ko kuwa zaki iya mana magana a shafin sharhin mu.
Share your feedback