Hanyoyi guda biyar da zai taimaka kada ki datti da kayan ki a lokacin al’adan ki

Ba lalai bane sai wani ya sanni lokacin da kike fara al’adan ki

Dattin jini a lokacin al’ada na kunyatar da mutum

Ga hanyoyi guda biyar da zai taimaka ki kauce shi

Ki samu kalanda
Hanya daya da zaki iya kauce tabon jini a lokacin al’ada shine ki san lokacin da al’adan ki zai zo. ki samu kalanda sai ki maki ranar da kika fara al’adan ki. Ki maki ko wanda rana da kika ga al’adan ki. ki maimaita shi a al’adan ki na gaba. Bayan kaman watani uku zuwa hudu na yin haka: sai ki kirga ranaku daga ranar da kika fara al’adan ki da ranar farko da zaki ga na gaba. Zaki ga cewa ranaku iri guda ne tsakanin al’adan ki a ko wanda wata. Ana kiran wannan kawanyan jinin halitan ki.
Misali, Binta ta kirga wai galibi ranaku ishirin da shida ne tsakanin ranar farko na al’ada da ranar farko na al’ada na gaba. Da al’adan ta ya fara a wannan watan, ta kirga ranaku ishirin da shida a kalandan ta. A ranar ishirin da shida ne al’adan ta na gaba zai fara. Zaki iya gani cewa naki ma ranaku ishirin da shida ne kaman na Binta ko kuwa zai iya zama ranaku ishirin da takwas ko ranaku talatin. Duk lambar da kika samu shine abinda zaki amfani ki san ranar da zaki fara al’adan ki na gaba

Ki saurare jikin ki
Kowane jikin mace daban ne. Wasu mata na samun kurajen fuska kafin al’adan su. Wasu kuma na samun ciwon ciki ko bakin ciki. Idan al’adan ki na gaba yazo, ki tuna da abunda ya faru da a na baya. Me kika lura? A lokaci na gaba idan kika ji wadanan abubuwan, zaki san cewa al’adan ki na nan zuwa.

Rufe kanki yanda ya kamata
kodai kina amfani da audugan al’ada ko kyale, ki tabata ya rufe wajan dake zub da jini. ki sanya duk abinda kike amfani da kyau a kampai ki saboda bazai matsa ba idan kina tafiya.

Ki canza audugan al’adan ki a koda yaushe
Ki canza audugan al’adan ki ko kyale da kike amfani da sauri kada ya jike. Dan tsira, ki canza a bayan ko wanda sa’o’i shida. Ki tuna dai, idan kika ji kaman kin jike, sai ki canza.

Ki samu wani ra’ayi
Ki tabata kina da wani audugan al’ada ko kyale a jakan ki idan zaki fita daga gida. Zai taimaka ki kauce datti da kayan ki da jini idan kika fita.

Al’adan ki bai zuwa da sauri ko kina masaniyan jini mai zuwa da gaggawa? Kiyi wa wata babba magana ko wani mai aiki a asibiti akan wannan abun.

Share your feedback