ki samu gaskiya akan al’ada
Al’ada abun da ake samunsa a dabi’ance ne kuma ba abun jin kunya bane. Ba abun dati bane. Ba ciwo bane.
Amma sauda yawa kina jin iri irin abubuwa akan al’adan ki. Wasun su gaskiya ne. Da yawan su kuma ba gaskiya bane. Ga wasu abubuwa da bai kamata ki yarda da ba:
Macen da take al’ada baza ta iya daukan cika ba
Wannan ba gaskiya bane. Maniyyin na iya zama a cikin jikin mace har zuwa kwanaki biyar. Idan mace tayi jima’i a karshen al’adan ta zata iya daukan ciki.
Kin zub da jini da yawo saboda haka, baza ki iya yin aikacen da kika saba yi ba
Lokacin gaba dayan al’adan ki, baki zub da jini da yafi ma’aunu arba’in (40ml). Wannan ma bai kai rubu’i na ledan ruwa guda ba. Zaki iya cigaba da rayuwar ki yadda kika saba.
Ciwon jinin haila ba abun da ake samunsa a dabi’ance bane, na ruhaniya ce
Ana samun ciwon jinin haila idan mahaifar ki ya matse dan ya zubar da tubalin sa. Ciwon na da zafi sosai. Kiyi magana da wata babba da kika yarda da akan yadda zaki kula da shi.
Jinin haila daban ne da asalin jini.
Jinin hailan ki daya ne da asalin jini. Jinin da kike samu a al’adan ki daya ne da wanda kike samuwa idan kika yanki hanun ki.
Akwai wasu irin abincin da bai kamata ki ci idan kina al’ada
Abincin da kike ci baya wucewa ta mahaifa. Yana wucewa ta ciki ne. Babu wani tabbaci cewa wani irin abinci na shafin hanyoyin hailan ki. Duk da haka gishiri da yawa a abinci zai iya sa ki kumbura da kuma abinci marasa amfani. Shawarar mu shine ki ci abinci mai bada lafiya idan kina al’ada.
Akwai tafarki da aka gaya miki akan al’ada? Ki gaya mana yau a shafin sharhin nan can kasa.
Share your feedback