Basu bambanta da juna ba sosai
Sunana Saratu, shakaru na goma sha shida, kuma ni na farko a gidan mu. Yan uwa na tagwaye ne da shekaru goma sha biyu da ake kira- Hassan da Hussaina. Ina kaunar su sosai. Kuma koda yaushe ina kokarin nuna musu cewa zasu iya dogara dani.
Saboda haka, kuyi tunanin farin ciki na da Hussaina ta yanke shawara ta nema shawarta da ni.
Har yanzu ina iya tuna da ranar daya faru da kuma yadda ta zo ta same ni da damuwa a fuskan ta.
Tana son ta san abun dake faruwar da ita. Bata gane canjin dake faruwa a jikinta ba. Tana bukatar bayyyani akan dalilin daya sa take fin tagwayar ta girma. Ta tsorata.
Sai na gaya mata;
Hussy, kinga abun dake faruwa dake? Ya faru da ni ma. Kuma ina shekarun ki daya faru. Na tsorata sosai. Sanda ya dauke Mama ta mun magana kafan hankalina ya kwanta.
Mama ta gaya mun cewa abun da nake masaniya shine ake kira Balaga. Abu ne da yan mata da samari ke masaniya idan suna girma.
Koda yake dukkan su na masaniyar canji, duk da haka mai yiwuwa ba zai faru da kowa a lokaci daya ba. Ki kalle kanki da Hussaini misali.
Wani abu kuma da ta gaya mun shine wannan canjin ba daya bane wa yan mata da samari.
Canji kamar girman nonuwa ko jinin al’ada a yan mata ko kuwa mafarkin jima’I da kuma zurfin murya wa samari.
Amma akwai canjin tsakanin yan mata da samari dake kama. Canji kamar canjin halayye, gashi a hammta ko kuwa a gaba.
Saboda haka ki shirya!!! Zaki kara ganin canji fiye da wadannan. Amma kada ki damu. Ba komai bane.
Hankalin yar uwata ya kwanta bayan nan. Kuma naji dadi dana iya taimakon ta a matsayin babban yaya.
Bayan makonni kadan, wani dan uwan mu daya girme Hassan da Hussaina da shekara daya ya zo gidan mu. Hussaina ta lura cewa muryan sa nada dan zurfi kadan.
Ta fara al’ajabin dalilin daya sa muryan Hassan bai yi zurfi Kamar na dan uwan mu ba. Da ta gaya masa, sai ya dan ji kunya. Sai na gaya mata abun dake faruwa.
Bayan nan, suka yi tambaya akan abubuwa da yawa kuma na iya kokari na na bayyana musu komai.
Yana da kyau da muka yi wannan maganar saboda Yanzu, tana taimakon Hassan shirya nashi canjin jiki.
Masaniyar canji kamar wannan ba komai bane. Kuma yana da kyau kuyi Magana akan sa a wani dake kusa daku, kamar abokai, ko wani dan iyalin ku ko kuwa amintaccen babban mutum dake da kwarewar.
Kuna al’ajabin yadda zaku fara maganar? Toh ga wasu dabaru; ku kwantar da hankalin ku kuyi Magana, ku bayyana tambayoyin ku, kuma ku saurara sharawar mutumin. Kuna da wasu Karin dabaru? Ku rarraba damu a sashin sharhin mu.
Share your feedback