Maslaha na gida guda biyar domin ciwon ciki na al’ada

Ku kasance da karfi da kuma lafiya

Al’ada na iya zuwa da zafi. Cikin ku zai ta ciwo. Baza ku iya motsa jiki kamar yadda kuka saba. Kuma, halayyar ku zasu canza.
br> Duk da haka, akwai abubuwa da zasu iya saka al’adar yazo da sauki. Kuma suna nan a gidajan ku! Kuna al’ajabin ko menene wadannan abubuwan? Ku cigaba da karanta domin ku gano.
br> Shayi
Kofin shayi mai zafi zai iya warkar da ciwon ciki al’ada. Ku gwada shan sa so biyu a rana – Da safe da kuma dare idan zaku iya. Wannan zai sassauta muku ciki kuma ya saka ku walwala.
br> Tawul mai zafi ko kwalban ruwa
Ku cika wani kwalba da ruwan zafi. Sai ku matsa shi a cikin ku da hankali (ko a bayan ku) har sai zafin ya ragu. Kuma, zaku iya zuba ruwa kadan a cikin tawul. Sai ku matsa shi a kan cikin ku (ko bayan ku). Wannan zai sanya gabobin mahaifan ku suyi laushi, ya saka ku walwalawa. Kawai ku tuna kada ruwan yayi zafi sosai.
br> Motsa jiki
Kuna mamaki? Kada ku damu! wasannin motsa jiki masu sauki kamar yin tafiya, ko mikar da jiki na sassauta ciwon ciki. Saboda haka, kuyi tafiya a cikin mahadin ku ko ungwan ku. Ko kuwa ku mikar da jikin ku a kasa a gida. Zaku yi mamakin yadda zaku ji dadin jikin ku.
br> Ku ci abinci masu kyau
Ku guje abubuwa masu sikari, da mai, da gishiri. Zasu iya kara saka ku kumbura da kuma canza halayyar ku. Maimako, ku gwada ‘ya ‘yan itatuwa da kuma ganye. Misali, ayaba zai taimake gabobin ku su huta kuma ya inganta halayyar ku. Kankana na samar da sinadaran gina jiki da zai warkar da gajiya. Lemu na cike da alli dake saukake ciwon ciki da kuma tashin hankali. Abu daya kuma: ku sha ruwa sosai.
br> **Wanka da ruwan zafi
Idan zaku iya, kuyi wanka da ruwan zafi. Zai warware gabobin jikin ku. Kamar haka, tiririn zai bude ramukkan fatan jikin ku, zai farfado daku daga ciki zuwa waje. Ku gwada duk sanda kuke so.
br> Kun taba gwada wani maslaha na gida domin ciwon cikin al’ada? Ya ya kasance? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback