Wadannan dabarun zasu iya taimakon ku
Kuna fafutukar natsuwa? Kuna ji kamar kuna bukatar wani abun zaki ko abun taunawa koda yaushe domin ku tsaya a farke?
Lokaci ya kai da zaku yi wasu canji domin ku kara inganta kanku.
Ga wasu dabaru da zaku iya gwadawa.
Kwakwalwa abincin karin kumallo na
Domin fara ranar ku da kyau, kuna bukatan abincin karin kumallo cike da sinadaran cikin abinci.
Zaku iya sanya pate, ko abincin da ake yi daga hatsi, ko burodin alkama, ko madara da kuma ‘ya ‘yan itatuwa a cikin abincin karin kumallon ku.
Kada kuyi kishin ruwa
Jikin ku da kuma kwakwalwar ku na bukatan isashshen ruwa.
Idan baku sha isashshen ruwa ba jikin ku zai gaji da wuri.
Ku guje kayan sha masu zaki kuma ku sha ruwa sosai.
Kwakwalwar ku zai muku godiya anjima.
Ku samu ma’adanin kimiyya
Tunani mai kyau nada muhimmanci idan kuna son kuyi koyo.
Hanya mafi kyau da zaku taimake tunanin ku shine da sinadarin lafiya da ake kira ma’adanin kimiyya. Kuna samun su sosai a nama, ko wake da kuma aleyahu.
Idan kuna son kuyi tunani mafi kyau, ku tabbata cewa kun ci wadannan abincin.
Kifi nada muhimmanci
Kifaye iri-iri nada mai dake da muhimmanci domin bunkasar kwakwalwa.
Ku gwada cin kifi koda yaushe.
Idan baku son kifi ko kuwa baku da hanyar samun sabon kifi, na gwangwani ma nada dadi da lafiya.
Ko kuwa zaku iya samun irin wannan taimakon kara karfafa tunani a madara da kuma kwai.
Kuna da wasu hanyoyi da zasu karfafa kanku? Rarraba da mu a sashin sharhi.
Share your feedback