Ku cigaba da tafiya, kuyi farin ciki

Hanyoyi masu nishadi da zaku kara lafiyar jikin ku

Wasan motsa jiki nada muhimmanci. Zai iya kara muku lafiya, da farin ciki da kuma karfi.

Wasan motsa jiki zai iya taimakon mu kara jin dadi da kuma kyau. Wannan zai iya karfafa tabbacin mu.

Koda ace kuna aiki sosai kuma baku da lokacin yin wasan motsa jiki.

Ga wasu dabaru da zai taimake ku fara aiki

Yin rawa idan kuna saka kaya
Idan kuna saka kaya, ku kunna wakan nan da kuke so. Kuyi rawa kamar babu mai kallon ku. Zaku yi mamakin yadda zai karfafa ku.

Idan ana nuna tallace-tallace a talabijin ku riga motsa jiki domin ku samu tsoka
A lokaci na gaba idan kuna kallon talabijin da abokan ku ko kuwa yan uwan ku, ku kalubale su kuga wanda zai fi yin tsalle a lokacin tallace-tallacen.

Taimakon aikin gida
So nawa ake tambayen ku ku taimaka da aikin gida?

Mai yiwuwa kuna jin gajiyar yin shara, ko goge kasa. Toh ku wayance ku ga tsin-tsiyar ko sandar goge kasar kamar reno ko kuwa na’urar garaya. Kuyi wani waka da kuke so.

Aikin ba dadi kawai zai yi ba, amma zai cikka jikin ku da sinadarin jinsi dake saka mutum jin dadi – wannan na hana mutum jin bakin ciki.

Ku aijye wayoyin ku
Ku bawa yatsun ku hutu kuyi magana da abokan ku fuska da fuska.

Kuyi tattaki a yayin da kuke labari da abokan ku.

Yin dariya da abokai a yayin da kuke shan iska zai saka ku jin dadi, kuma zaku mike cikin ku da tsokan kafan ku. Wannan yafi komai dadi.

Renon yara
An taba saka ku duba yaron dan uwar ku ko na makwaftar ku?

Ku kalubale su suyi wasanni masu nishadi kamar boji boji.

Zaku iya koya musu wani wasa da kuke son yi da kuke kananan yara.

A ta nan zaku motsa gabobin jikin ku.

Ba sai kun je dakin motsa jiki ba domin ku samun isashsahen lafiya.

Kun san cewa samun lafiyar jiki zai kara saka ku samun tabbaci da kanku.

Kuna da sauran dabaru akan yadda zaku samu lafiyar jiki? Ku rarraba da mu a sashin sharhi.

Share your feedback