Kun duba sa a google?

Labarin bincike na yanar gizo gizo

Ekaite ta rikice. Tana kasuwa tana taimakon maihaifiyar ta. Wani likita na yin wa yan kasuwa magana akan wani cuta. Kuma bata fahimce yawancin kalmomin ta ba.

Ta juya ta tambaye yaron dake gefen ta ma’anar “kwayar halitta”. Sai yace mata, “kina rike da waya a hanun, ki bincika a google”. Ya fadi da rashin hakuri. Ekaite bata gane abun da yake nufi ba. Menene “google?”

Tana yawan amfani da wayan mahaifiyarta ta kira mutane. Yar uwar ta ta nuna mata yadda zata yi amfani da Facebook.

Ta kalla wayan sai da danna jan mabudin mazabar. Bata amfani da dukka abubuwan nan, tayi ajiyar zuciya.

Gashi nan! Google. Abun da yaron ya fadi kenan. Ta latsa a kan tambarin mai launi. Bada jimawa ba wani akwati ya fito da kalman bincika a cikin sa. Sai kuma ta lura cewa akwai wani “akwatin bincike” tare da alamar Google a samar mabincikar bayanai wayan.

Zata iya binciken komai? Ta rubuta kalman, “Kwayar halitta”. Nan take, wasu jerin kanun abubuwa suka fito. Daya yace,”menene kwayar halitta?” Wannan ne hakika abun da ta tambaye kanta. Makalar yayi mata bayani cewa kwayar halitta ne dan karamar na’urar rayuwa. Dukkan mu nada kwayoyin halitta a jiki.

Ekaite ta cigaba da sauraro. Tana murna yanzu saboda ta san akan abun da likitan ke magana akai.

Da zaran ta kai gida, ta gama aikin ta na gida. Sai ta tambaye mahaifiyarta ta bata wayan ta kuma.

Menene abun nan da nake ta son na sani? Ta rubuta “Kurajen fuska” a wajan bincika. Wani makala ya fito mai bada dabaru akan kawar da kurajen fuska da abubuwa masu arha kamar lemun tsami da kuma sikari.

Ekaite taji dadin binciken kalmomi daban-daban. Musamman kalmomi dake dangantaka da jikin ta. A da tana jin tsoron yin wa wani maganar jikin ta. Ta koya cewa yan mata da yawa na yin al’ada a kwanaki uku kawai kamar ita. Dukkan yan uwanta mata na yin al’ada na kwanaki shida. Wannan ya saka ta kasancewa da damuwa.

Ekaite tayi wa mallamar ta magana so daya akan safgar ta. Mallamar ta ta bata shawara ta cigaba amma kuma ta bata kashedi akan wasu shafukkan yanar gizo gizo dake bada bayanai mara kyau. Bayan taji wannan, Ekaite ta tabbata ta karanta shafukkan yanar gizo gizo da yawa idan tana binciken wani darasi. Idan dukkan shafukkan yanar gizo gizon suka fadi abu daya, zata kara yarda da bayanai.

Kuma tana son duba yanar gizo gizo daga wani sanannen kungiya. Ta yarda da shafukkan yanar gizo gizo daga sanannen jaridu da kuma mujalla. Amma ta tabbata tana tamabayar wani likita akan matsalolin lafiyar jiki. Yanar gizo gizo ba likita bane.

Ekaite ta koya abubuwa da yawa daga amfani da waya. Akwai wasu abubuwan aiki a wayoyi da kuke so ki kara koya akai? Kawai ku tambaya a wajan sharhi.

Share your feedback