Kuna da abokai mafi kyau da zuku iya dogara ga?

Abokai na na goyan baya ba.

Sannu! Sunana Amina, kuma ina da abokai biyu da sunnan Mariam da kuma Halima. Babu kamar irin su.

Kwashe lokaci dasu a karshen mako abun al’ada ne a wajan mu, musamman a ranar sati da muke samu muyi kallon wasannin kwaikwayo a gidan inna na.

A daya daga cikin wadannan satin ne wani abu ya faru.

A wannan satin, da ni da abokai na na hanyar zuwa gidan inna na kamar yadda muka saba domin muyi kallo a katon talabijin din ta. Halima tace mu kama hanya zata sadu damu domin tana son ta biya mai kitson ungwan mu kudina ta. Bamu yi nesa ba kafan muka ji Halima na ihun suna na. Muka juya muka ga tana guda ta same mu. Da ta kai wajan mu ta rada ta gaya mun “Amina, kina zub da jini!”

Ta mika hannu ta nuna mun wajan da jinin yake, sai na duba naga babbar jan tabo a kan riga na. Na fara al’ada na.

Naji kamar kasa ya bude ya hadiye ni.

Na fara al’ajabin lokacin da nake ta tafiya da tabon jinni a riga na. Naji kamar nayi kuka, amma abokai na suka lallashe ni suka ce, da mutane sun gani da sunyi mun Magana. Tun da dai, ungwan mu karami waje ne, kuma kowa ya san kowa.

“Mutane na aikin gaban su, baza su kalla rigar ki ba Amina! Kuma, abu ne da aka saba dashi ba wanda zai hukunta ki”, Inji Mariam. Halima ta bani gyale na daura a kwankwaso na domin na rufe dattin. Sai, taje wani shago ta siyo mun auduga.

A yayin da muke jiran Halima ta dawo, Mariam ta gaya mun wani babban sirri. Tace ta fara nata al’adar a watani shida da suka wuce. Tace ta tsorata da farko amma yar uwar ta ta taimake ta ta koya mata cewa al’ada abu ne da aka saba dashi kuma kada ta ji kunya.

Ina godiya ga aboaki na. Bana son nayi tunanin abun da zai faru da basu nan dani a lokacin da abun ya faru.

Da Halima ta dawo da audugan, tace mun “Amina, wannan abun al’ada ce wa yan mata. Kada ki damu, komai zai daidaita”.

Kuma da gaske ne – na warware!

Menene labarin al’adar ku?

Share your feedback