Yadda zaku guje rashin lafiya
Ku guje kwayoyin cuta
Kowane rana muna buda kanmu wa kwayoyin cuta. Kwayoyin cuta ne abubuwan nan kamar bakteriya da kuma kananan halittar cuta dake saka mu rashin lafiya.
Zasu iya bazawa ta zufa, ko yawun da kuma jini. Wasu na iya bazawa daga mutum zuwa mutum.
Ga wasu hanyoyi da zaku iya gujan wadannan kwayoyin cutar.
- Ku guje zuwa kusa da mutane. Inda yiwuwa ku kuje mutane dake da mura, ko tari, ko kuwa tarin fuka. Idan kuna cikin wani daki ne, kuyi kokari ku bude tagogi domin ku samu iska. Idan kuka taba kayan wasa, ko kuwa kayan girke-girke na wani da yayi ciwo ba da jimawa ba, kuyi kokari kuyi wanka ko kuwa ku wanke hanun ku bayan kun bar wajan.
- Ku wanke hannayen ku. Wannan ne hanya mafi kyau da zaku kore kwayoyin cuta. Ku wanke hannayen ku koda yaushe bayan kunyi amfani da shadda. Ku wanke hannayen ku kafan kuci abinci.
- Ku kara wa kanku lafiya ta cin abinci masu kyau, yin wasan motsa jiki sosai da kuma samun isashshen bacci. Dukka wannan zai kara karfafa garkuwar jikin ku. Zai taimake jikin ku kashe kwayoyin cuta.
- Ku zub da fale-falen takardar da kuka yi amfani da. Kada ku tara fale-falen takardar da kuku yi amfani da a kusa da gadon ku ko a kan teburin ku. Zasu iya jawo kwayoyin cuta. Ku zub da su da zaran kuka gama amfani dasu domin ku guje baza kwayoyin cuta wa sauran mutane.
- Ku rufe bakin ku da bayan hannun ku idan zaku yi tari ko atisahwa. Kada kuyi tari ko atishawa a cikin tafin hannun ku.
Idan kuna rashin lafiya ko kuwa kuna tunanin akwai abun da bai dace ba, kada ku jira. Kuje wani asibiti dake kusa daku.
Ku gaya mana wasu hanyoyi da zaku kore kwayoyin cuta a wajan sharhi.
Share your feedback