Yadda zaku samu lafiyayar gashi

Ranakun gashi mai kyau koda yaushe

Lafiyayar gashi. Wasun mu nada shi. Wasun mu na so– kuma babu abu mara kyau da shi.

Don haka, kun shirya samun gashin nan da kuke so? Gashi nan:

Ku yanke bakin gashin
Kun san wadannan tufkan gashin ku daya warware? Ana kiran su lalataccen bakin gashi. Idan kuka yanke su, gashin su zai kara cika, da kuma walkiya. Zai kara tsawo da karfi. Bani biyar, yarinya!

Wanda aka yi a gida
Wasu lokuta abun da kuke nema na nan a cikin madafar ku. Ku fasa kwai a cikin wani kwano. Ku saka madara kadan, da cokali biyu na man zaitun, da kuma ruwan lemun tsami. Ku juya su tare sai ku shafa a gashin ku. Mai yiwuwa gaurayan ya samu wani wari mai karfi amma ba komai. Ku barsa a gashi ku na minti ishirin zuwa talatin, sai ku wanke. Kuyi wannan so daya a wata.

Komai akan danshi
Man zurman nada kyau wa lafiyar gashi. Ku saka a cikin gashi ku so biyu ko uku a mako. Ku maida hankali a wajan da akwai matsala kamar gaban gashin ku. Man kwakwa da man kade nada kyau wa danshi ma. Ku gwada su kuga wa kanku. Zaku iya samun su a shagon ungwan ku ko kuwa a kasuwa.

Sauki yafi
Abubuwa yan kanana ne ke kawo canji. Ku taje gashin ku da hankali. Ku matsa fatan kan ku da hankali. Kada kuyi amfani da roba ko kuwa kowane kayayyakin ado mai kaushi a gashin ku. Ku rufe kanku da wani dankwali mai laushi kafan kuyi bacci. Kuyi bacci a kan matashi mai laushi. Dukkan wannan zai hana gashin ku karyewa.

Kuci abinci masu kyau
Inganta irin nau’in abincin da kuke ci zai taimake gashin ku. Kuma abu mafi inganci? Dukkan jikin ku zai amfana daga wannan! Dankalin hausa, kwayan hatsi, madara da kuma ganye na cike da sinadaran kara lafiya dana gina jiki. Zasu tada hujin fatan gashin ku, kuma su baku lafiyayar gashi.

Ku tuna kuyi hakuri. Samun lafiyayar gashi na daukan lokaci. Ba zai faru nan take ba. Saboda haka ku kwantar da hankalin ku ku more wannan tafiyar. Muna saka rai a kan ku.

Kuna da wasu dabarun samun lafiyayar gashi? Gaya mana a wajan sharhi.

Share your feedback