Audugan jinin al’ada na sun kare!

Naomi ta same kanta a wani matsala

A ranar farkon jarabawa na, na tashi da kwanciyar hankali da farin ciki. Nayi karatu sosai, ina nan a shirye. Na wanke hakora na, nayi wanka. Sai naji wani abu na gangaro kafa na. Na duba kasa kuma kamar yadda nayi tunani, jinin al’ada na ya zo.

A daki na, naga cewa audugan al’ada na ya kare. Bani da isasshen kudin siya wani. Kuma bana son nayi makaran zuwa jarabawa na. Sai na yanke sharawa na saka riga mai kauri naje makaranta.

Na gama Jarabawana na farko babu matasala. Amma can da rana, naga na jike sosai. Ina bukatan yiin canji da wuri. Amma matsalar shine ina kunyar tambayen taimako. Bamu maganar al’ada a makaranta. Wani babban abun kunya ne. Bana son a hukunta ni.

Duk da haka, bani da isasshen lokaci. Dole nayi tunani da hanzari. Na gaya wa kaina ba komai bane, al’ada ba abun kunya bane. Wata abokiyata zata ji dadin taimako na. Abu mafi munin shine kawai su ce a’a. Kuma idan suka yi, zan iya tambayen wani.

Na kirga daga daya zuwa goma a kai na, sai na je. Na same abokiyata Efosa na tambaye ta ko tana da ragowan audugan al’ada. Kun san me tace? Eh!

Efosa ta bani auduga guda uku. Naji kamar nice yarinya mai sa’a a gaba dayar duniya. Na gaya mata naji tsoron yin mata magana da farko. Ta gane. Ta gaya mun cewa a da tana kunyar jinin al’ada ita ma, har sanda ta koya cewa al’ada ce na girma. Kamar kara tsawo da girman nonuwa.

Na gama jarabawana na biyu babu matsala. Na samu sukuni- kuma naji dadi da ban saka tsoro ya hana ni ba. Na yanke shawara cewa nan gaba idan na shiga wani matsala, ba zan damu da abun da mutane zasu yi tunani ba. A maimako, nayi wa kaina alkawari cewa zan fara ajiyan kudi na audugan jinin al’ada. A ta nan, koda yaushe zan samu ragowa idan ina bukata.

Kun taba samun kanku a al’amarin nan? Me kuka yi? Kada ku boye, yan mata. Ku gaya mana a nan kasa.

Share your feedback