Hayaniyar al’adar Itunu

Yadda yin tunani da sauri ya ceta ranar!

A ranar shagalin kade na al’ummar mu ne, kuma ina ta murna. Ina cikin kungiyar masu wasan kwaikwayo. Na kosa na nuna wa kowa kwarewa na na wasan kwaikwayo.

A wasan ni ce wannan fitinaniyar mikiyar mai wayo daya rude wani mafarauci domin ya ceci masarautar dabbobin.

A sa’a kafin na hau samar dakalin, na fara jin ciwon ciki.

Na zata tsoron fuskanta jama’a ne ko kuwa wani abu dana ci a baya.

Duk da haka dai, na gaya wa kai na cewa ina da wasan yi kuma bazan bar kowane abu ya hana ni ba.

Sai lokaci ya kai da zan hau dakalin. A nan ne asalin hayaniyar ya fara. Ina kan hawa samar dakalin sai naji wani abu mai dumi na gangaro kafafu na.

Wayo Allah...na fara fargaba. Al’ada na ya zo. Na rikice ban san abun yi ba. Munin al’amarin shine, na saka matsatstsen kaya.

Ina bukatan wani dabara idan bana son gabadayan yan al’ummar mu su ga jinin haila na.

Sai da lokaci na ya kai, na yanke shawara nayi wani abu dabam.

A maimakon tashi a kan mafaraucin domin na sake dabobbin, na yanke shawara nayi tsalle na shiga cikin wani tunkunyar abinci domin na janye hankalin sa.

Ko da yake wannan baya cikin labarin, nayi wa masu taimako na ihu daga cikin tukunyar. “ Dan Allah ku dauke ni ku kai ni samar tudu. Zamu halaka tukunyar mafaraucin kafan ya juya ya zamar damu abincin sa!”

Sauran masu wasan suka dan rude, amma sai na kama idon kawa ta na bata kallon damuwa.

Da sauri ta kira masu taimakon dabbobin, sai suka dauke ni daga dakalin da wuri.

Na gaya wa Sarah abun daya faru. Ta rungume ni tace kada na damu, saboda jinin al’ada ba komai bane. Ta ja ni bandaki sai ta gaya wa sauran mutanan su cigaba da wasan. Ta bani auduga, da gyale na rufe riga na.

Na kama fikafikai na na ruga zuwa dakalin, sai na shiga shagalin karshen wasan.

Da godiya ga saurin tunani na da kuma taimakon abokiyata, na tsira hayaniyar al’ada na.

Wasu lokuta al’adar ku na iya zuwa a lokacin da baku shirya ba kuma ba komai bane. Amma kamar Itunu, abun da kuke bukata shine samun hanyar da zaku kula da matsalar da wuri.

Ku tuna, al’ada abu ne da aka saba da, kuma ba abun kunya bane!

Kun taba masaniyar wani hayaniyar al’ada? Ku rarraba labaran ku da mu a sashin sharhi.

Share your feedback