…..Sai abinci mai kara lafiya ya shiga!
Mu mata jikin mu na cinye kuzari sosai. Shiyasa muke yawan son wadannan kayan dadin kamar biskit da lemun sha masu sikari.
Gala da La Casera nada dadi sosai. Amma basu da kyau sosai ma girman jiki.
Tun da wuri ki guje tarkacen abinci da lemun kwalba mai sikari sai ki fara cin abinci mai kara lafiya.
Meyasa zan ci abinci me kyau?
Cin abinci mai kyau ba akan nauyin jikin ki bane. Akan lafiyar ki ne. Zaki iya cin kowane irin abinci kuma baza ki kara nauyin jiki ba.
Saboda kina kan girma, jikin ki na bukatan sinadaran cikin abinci sosai.
Ya kamata ki ci abinci mai kara lafiya domin ki samu sinadaran nan. A ta hanyar nan ne kawai zaki kara wa jikin ki da tunanin ki karfi.
Maye gurbin lemu mai sikari da ruwa
Mun san cewa ruwa ba wani abu mai nishadi bane ko burgewa. Amma yana da kyau a jikin ki. Yana da muhimmanci a lafiyar jikin mu. Ruwa na rike da sitin bisan dari a jikin mu. Muna zub da ruwa sosai daga jikin mu a rana. Daga zufa, yin fitsari, harda yin nunfashi ma.
Kina ji kamar ruwa bai da dadi? Ki kara masa dadi da ya ‘yan itatuwa ko lemu.
Cin abinci mai kara lafiya kyauta ne ma jikin ki.
Baki yi wa wani, kina wa kanki ne.
Kina da jiki guda ne! kiyi kaunar sa kuma ki kiyaye shi da lafiya!
Share your feedback