Ki san abubuwa dake faruwa da jikin ki

Amsa wasu sanannen tambayoyi akan jikin ki

Wasu lokuta muna bukatan amsa, amma bamu san wanda zamu tambaya ba.
Wasu lokuta mun san wanda zamu tambaya, amma bamu san yadda zamu yi ba.

Domin taimakawa, ga wata likita da sunan Dr, Blen zata amsa wasu tambayoyin ku da kuke yawan tamabaya.


Ni budurwa ce har yanzu? Na gamsar da kai na ta hanyar yin wasa da al’aura na amma jini bai fito ba.

Na farko, zub da jini ba alamar budurci bane. Akwai wasu budurwai da basu zub da jini ba bayan suka yi jima’i. Wannan baya nufi cewa su ba asalin budurwai bane. Saboda haka, kada ki hada budurci da jinin da kike gani bayan kowane abu daya kutsa cikin farjin ki. Wasu aikin motsa jiki masu wuya (ana ganin irin wannan a tsakanin mata masu wasanin motsa jiki sosai).


Al’ada na baya zuwa yau da kullun; yana yawan zuwa ba zato ba tsammani kuma yana kunyatar da ni. Dan Allah ku taimaka

Samun al’ada da bai zuwa koda yaushe ba komai bane. Gaskiya maganar shine, akwai mutane da yawa dake samun al’ada da bai zuwa koda yaushe. Yadda zaki guje kunyatar kanki ko yin datti da kayan ki shine ki samu kalanda (daya daga cikin biyun nan, a cikin wayan ki ko a kalanda da zaki iya saka wa a aljihun wandon ki da zakiyi maki al’adan dan ki shirya zuwan shi na nan gaba. Ki samu wani karamin jaka da zaki ringa saka audugan al’adan ki saboda idan al’adan ki yazo kina nan a shirye.


Ina yawan ganin wani abu mai launi a kampai na kuma ba jini bane. Ina tsoro. Ban da lafiya ko wani abu ne
Ana kiran sa launi mai ruwan madara ko kwai dake fitowa daga farji, kuma kowane mace na ganin sa. Yana canza lokaci daban daban na Kawanyar jinin hailan ki; sarai da kuma mikarwa- kuma dai ana kiran wannan magunya mai hayayyafa kuma yana nuna cewa kina saukar da kwai. Sarai kuma kamar ruwa- wannan baya zuwa a takamammen lokaci. Yana iya zuwa a kowane lokaci a Kawanyar ki. A launin ruwan kwai ko na kore- wannan yana nuna cewa akwai alamar kamuwar cuta. Launin kasa- mai yiwuwa ya faru bayan al’adan ki kuma an san cewa zai wanke farjin ki. Yana kama da launin kasa domin an san tsohon jini na da kamanin launin kasa. Lokacin daya kamata ki damu akan mugunyan ki shine idan yana da launin kore ko mai kama da ruwan kwai, idan yana da kauri kamar cuku, idan yana da kamshi mara dadi, ko kuraraje, da kuma kumbura idan yana kaikayi. Idan kina masaniyar daya daga cikin wannan alamun, mai yiwuwa kina bukatar ganin likita nan take.

Me ke sanadin kurajen fuska kuma wanda abinci ne zan ci domin na kauce samun kurajen fuska?
Ana hada kurajen fuska da sarrafan mai, da kwayar halitta na fata da suka mutu, da buda na fata daya toshe kuma wasu lokuta kamuwar cuta na kananan halittu. Abubuwa da yawa zasu iya zama sanadin kurajen fuska daga damuwa zuwa sinadarin kimiyya wanda jikin mutum ke samarwa (wanda ake hadawa da al’ada) zuwa matashi ko zanin gado mai datti zuwa tabe taben fuskan ki kowane lokaci. Wasu lokuta, cin abinci me mai sosai zai iya jawo miki kurajen fuska. Duk da haka zaki iya gujen kurajen fuska ta wannan hanyoyin: wanke fuskan ki so biyu a rana, ki tabata hanun da kumbunan ki nada tsafta kowane lokaci, ki wanke su da sabulu da ruwa. Ki guje fasa kurajen fuskan, ki daina taba fuskan ki, kuma ki goge dukka kwalliyan fuskan ki kafan kiyi bacci. Kada kiyi amfani da kayan kwalliya dake da ma’adanin kimiyya da zasu iya bata miki fata. Kuma, ki rage cin abinci me mai da silari. Kici abinci wanda yake sa mutum kasance cikin koshin lafiya kamar kifi da ganye. Ki wanke zanin gadon ki kowane lokaci kuma ki sha ruwa sosai.

Ya zan rabu da warin jiki?
Bidan kina son ki rabu da warin jiki, ana baki Shawara ki amfani da sabulun wanka wanda zai kore kananan halittar nan masu jawo cuta. Kuma kiyi amfani da Tulare me kamshi da kuma kyau kowane lokaci. Kuma kiyi amfani da wear masu tsafta. Kaya da akayi daga audugan, ko gashin timkiya. Ki sa fata ki ya samu iska dan yana da kyau ma jiki.

Kina da karin tambayoyi ko damuwa? Gaya mana a shafin sharhin mu.

Share your feedback