Ku kali cikin madubi

Ku ga yadda hakika kuka gagarumi

Ku je madubi. Ku kala ciki. Me kuke gani? Kurajen fuska? Gashi da bata zama waje daya? Wani yanayin fata da baku so? Kuna gani kamar kuna son ku rage jiki? Kuna ji kamar sakaru? Mai yiwuwa kuna ji kamar ku ba cikakku bane.

Muna son ku daina dukkan wadannan tunanin. A maimako, ku san cewa ku kyawawa ne. Kuma ga dalilai....

Abun farko da zaku tuna shine baku kadai bane ke jin irin haka– Yawancin yan mata na fama da aunin darajar su. Abu na biyu da zaku tuna shine – Yakamata ku daina jin haka!

Gaskiya, ku daina wadannan tunanin mara kayu akan kanku yanzun nan!

Zamu iya zama ma’kiyayyan kan mu mafi muni. Muna yanke wa kanmu hukunci sosai. Muna yin tunanin da fadin abubuwa akan kanmu da baza mu taba tunani ko fadi akan abokan mu ba….ko kuwa makiyan mu.

Dukkan mu na bukatan hutu kuma mu fara koyan kaunar kanmu.

Labari mafi kyau? Zamu iya farawa yanzu.

Ku dauke wannan farkon matakin. Ku kara duba madubi amma yanzu, ina son ku ga kyakkyawan yan mata masu kyawawan zuciya. Kun sa waye ne? Ku ne.

Sai ku kara fadi kuma. Sai kuyi ihu. Kada ku damu idan mutane a gidan ku suna tambaya ko kuna da lafiya, ku cigaba da fadin sa.

Yakamata kuyi imani da shi, saboda gaskiya ne.

kyawu bata nufin abun da kuke gani a mujalla ko kuwa talabijin. Ba ra’ayin wani bane kuke kokarin bi. Ba akan abun dake waje bane kawai. Akan abun dake cikin zuciya ku ne.

Ku fada kuma: “ Ni kyakkyawa ce”

Saboda kuna da kyau. Baku cika goma ba, ba wanda ya cika. Amma zaku iya zama masu aminta. Zaku iya tabbata kanku. Zaku iya yanke shawarar yadda zaku ji ko kuwa yadda zaku amsa duniyar. Yana hanun ku, zaku iya gina gaba dayan rayuwar ku akan kalmomi guda uku:

“Ina da kyau a ciki da waje”

Kuma da zaran kuka sani a zuciyar ku, komai zai yi sauki. Baza ku kara bata lokaci akan tunani mara kyau. Ku mayar da hankalin kuzarin ku akan abubuwan da kuke so sai ku shirya rayuwanku na gaba mai kyau.

Gaya mana abun da ya saka ku kyau a ciki da kuma waje a wajan sharhi.

Share your feedback