Kuyi kaunar jikinku, yan mata!

An halicci ku da kyau

Eh ku! Kowane incin jikin ku na cancantar kauna, a ciki da waje. Koda ya girman ku ko siffar ku, kuna da kyau a yadda kuke. Siririya ko mai kiba, mai tsawo ko gajeruwa, kun isa.

Koda kun san cewa wannan gaskiya ne, wasu lokuta shaukin ku zasu mamaye ku. Tabbacin ku zai ragu, zaku fara kwatanta jikin ku dana sauran mutane. Zaku fara ji dama duwawun ku nada girma kamar na abokan ku. Kuma abun mafi mamaki? Mai yiwuwa abokan ku naji dama suna da irin siririn jiki kamar naku. Abun da hauka, amma gaskiyar kenan!

Al’ada ne ku so abun da baku dashi. Amma kada ku bari ya mamaye ku. Dukka jikunan mu sun banbanta kuma dukkan mu na musamman ne a yadda muke.

Duniyar zata iya muku wuya ku so kanku. Wasannin kwaikwayo da kuma mujalla sun nuna mana jikin nan mafi kyau. Idan jikin ku bai yi kama da wannan ba, mai yiwuwa kuyi bakin ciki. Mai yiwuwa ma ku fara kwatanta kanku da wata da baku sani ba.

Idan kuka samu kanku a irin wannan halin, zai yi sauki ku daina gamsuwa da kanku. Kuma abun da baku son ya faru daku kenan.

A maimaiko, ku rungume yadda kuke koda menene duniya ya fadi muku. Kuyi tunanin dukkan abubuwa masu kyau game da jikin ku. Yadda idannu ku ke walkiya idan kuna dariya. Yadda kashin ku ke motsi idan kuna gudu. Yadda da dai kawai kuka hadu. Sai ku daga kan ku sama ku cigaba da kaunar kanku. Koda yaushe ku tuna: Ku na musamman ne kuma kun cancanci kauna. Kada ku bari wani ya gaya muku dabam.

Idan kuka yi kaunar kanku, mutane zasu lura. Farin jini zai kewaye ku. Wasu mutane zasu bi da ku da hankali. Amma kuma wasu zasu yi muku mugunta. Zasu fadi abubuwa mara kyau akan jikin ku. Idan wannan ya faru da ku, kuyi kokari kada ku bari ya dame ku. Mai yiwuwa ra’ayin jikin nan mafi kyau ne ke tasirin wadannan mutanen. Saboda haka, idan suka ga wani da jiki dabam, suna fadin abubuwa mara kyau ba tare da sanin ko suna raunata mutane ba. Kada ku bari ayukan su ya dame ku. Aunin darajar ku baya kulle da ra’ayin kowa. Ba komai bane idan kowa na tunanin ko kuna da kyau ko baku da. Abun mafi muhimmanci shine yadda kuke ji game da kanku. Aunin darajar na asali na zuwa daga cikin zuciya ne.

Idan akwai wani dake saka ku jin bakin ciki game da kanku, ga yadda zaku bi da su: https://goo.gl/xRtDop

Kada ku manta: Wannan jikin naku mai kyau shine kadai kuke da. Kuyi kaunar sa da kyau.

Ya kuke nuna wa jikin ku kauna? gaya mana a nan kasa.

Share your feedback