Cikakken jagora na al’ada
Al’adar ki, ko bako na wata-wata, ko jinin haila. Koda menene kike kiran sa, Yawancin mu na ji dashi a kowane wata. Kuma yana iya rikitar dake. Mai yiwuwa baza mu iya gane abun dake faruwa ba. Toh ga abun daya kamata ki sani.
WANDA LOKACI YAKE FARAWA?
Yawancin yan mata na ganin al’adar su a tsakanin shekaru goma zuwa goma sha biyu. Wasu kuma na samun nasu a shekaru goma sha shida.
MENENE TSAWON LOKACIN SA?
Wa Yawancin mu ranaku uku zuwa biya. Amma zai iya kaiwa ranaku bakwai.
MEYASA YAKE DA ZAFI?
A kowane wata jikin ki na shirin daukan yaro. Yana yin haka ta kara kaurin bangon mahaifan ki. Sai ya sakar da kwai. Idan kwan bai nuna ba, wannan layin na yagewa. Wannan abun ne ke jawo zub da jini. Zafin na zuwa domin wasu lokuta mahaifan ki na daurewa idan ya yage layin. Al’ada ne idan kika masaniyar zafi.
YA ZAN BI DA ZAFIN?
Zaki iya gwada wasan motsa jiki. Wasu lokuta tafiya a hankali na aiki. Shan ruwa da shayi mai zafi na taimako. Ki gwada kwanciya kadan. Wa wasu mata zafin bashi da kyau, yana hana su yin aikace-aikace na kowane rana. Idan wannan ya faru, zaki iya zuwa asibiti domin ki samu magani.
ZAN IYA DAUKAN CIKI IDAN INA AL’ADA?
E, zaki iya daukan ciki. Zai iya yiwuwa ki masaniyar samuwar kwan halitta kafan ko kuwa a lokacin al’adar ki. Idan maniyyin ya hadu da kwan a irin lokacin nan zaki iya daukan ciki.
AL’ADA NA IYA SANADIN KARANCIN JINI?
Asalin al’ada na nan kamar cokali guda uku. Wannan iyakan jinin ba zai sa ace zai saka ki cikin hatsari ba.
AL’ADA NA IYA HANA NI YIN AIKACE DANA SABA?
Wannan amsar a’a ne. Al’adar ki ba ciwo bane. Idan yazo zaki iya cigaba da yin abubuwan da kika saba. Kije makaranta, ki je kasuwa, ki tuka keke, kiyi tsale, kiyi guda, zai iya ma yin rawa.
AL’ADA NA YA MAIDA NI KAZAMIYA?
A’a. Al’adar ki dai-dai yake. Kowane yarinya na masaniyar sa. Ba abun jin kunya bane.
Kina da sauran tambayoyi akan al’ada? Tambaya mu a shafin sharhin mu.
Share your feedback