Me zan yi?
Sannu Babban Yaya,
Ina ganin akwai wani matsala dani. Al’ada na baya zuwa kamar na abokai na. Wasu lokuta yana zuwa so biyu a wata. Sauran lokuta yana zuwa da makara. Wasu lokuta kuma bana ganin sa gaba daya. Kamar watan daya wuce!!
Na tambaye wasu abokai na. Sunce bai kamata ba. Ina tsoro. Ina ganin bani da lafiya.
Meke faruwa dani? Me zan iya yi? Ina jin tsoro.
Nagode
Anita.
Sannu Anita,
Babu dalilin rikicewa. Abun da kike masaniya shine ake kira sababbun al’ada. Kuma yana faruwa da yawancin yan mata. Kowane kowanyar al’adar mace ya banbanta (Kawanyar al’adar ki lokacin nan ne tsakanin ranaku na farko na al’adar ki). Al’adar kowane mace baya zuwa kamar yau da kullum a kowane kwanaki ishirin da takwas. Saboda haka, kada ki damu idan naki ya banbanta da na abokan ki.
Sababbun al’ada abu ne dake faruwa da wasu yan mata, musamman a shekarun da suka fara al’ada. Yawancin lokuta, sababbun al’ada na cikin canjin dake iya faruwa idan kina budurwa. Idan kika kara yin girma, yana yiwuwa kawanyar ki zai canza.
Abubuwa kamar rashin lafiya, kara ko rage nauyi sosai, gajiyan jiki ko kuwa yawan tafiya zai iya jawo sababbun al’ada. Wannan saboda wadannan abubuwan sun shafi yankin kwakwalwa nan ne dake tsare al’adar ki. Ba abun damuwa bane, yana faruwa.
Wasu lokuta, rashin daidaituwa na sinadarin jinsi dake jawo sababbun al’ada. Sinadaran jinsi ma’aiki ne dake iko da wasu ayyukan jikin mu kamar al’ada da kuma haihuwa. Saboda jikin ki na kan canzawa da girma, ba komai bane idan matakin sinadarin jinsin ki ya canza.
Amma idan baki ga al’adar ki fiye da watani uku ba, zaki fara girmar da gashi a fuskan ki ko kuwa a kan kirjin ki, al’adar ki zai zo da karfi kuma yawancin lokuta zai iya kai kwanaki bakwai, ko kuwa kiyi ciwon ciki sosai. Kije wajan wani likita a al’ummar ku ki duba kanki.
Wani abun muhimmanci kuma shine ki san yadda zaki shirya wa al’adar ki. Saboda sababbun al’ada, zai miki wuyan sanin lokacin da zaki sa ran ganin al’adar ki na gaba. Muna baki shawara ki samu audugan al’ada da yawa a jakan ki. Musamman idan baki gida.
Wata hanya da zaki tabbata cewa al’adar ki bai zo miki ba zato ba tsammani ba, shine idan kika lura da wasu canji a jikin ki. Canji kamar kurajen fuska, ciwon ciki, da kuma canjin halayye da sauran su.
Idan kina son ki kara koyan yadda zaki lura da al’adar ki, ki karanta labarin Bunmi a nan.
Ki kula da kanki kuma ki cigaba da yin mana magana.
Da godiya,
Babban Yaya
Share your feedback