Babban sirrin kwaliya

Ku gano yan kankanin abubuwan nan da baku taba sani ba

Sannu Springster!

Dukkan mu mata munzo a siffa, launi da kuma girman jiki daban-daban. Koda mai tsayi, ko gajeruwa, ko baka, ko fara, dukkan mu munzo a siffa na musamman. Muna da kyau a ciki da kuma waje.

Amma yana da kyau mu lura da kan mu idan muna so. Ba komai bane idan muka kula da jikin mu. Kuma akwai hanyoyi masu sauki da dabi’a da zamu samu wannan walkiyan. kun shirya ku fara? Muma mun shirya.

Kafa mai laushi
Bayan kunyi wanka, ku saka ruwan lemum tsami a cikin man shafawan ku. Sai ku shafa shi a gabadayan kafafun ku da hannayen ku. Bayan minti goma, ku bushar da fatar ku, shikenan kun gama.

Cikakken lebe
Kuna sha’awar cikakken lebe? Ku gauraya sikari da man geda a cikin wani karamar kwano. Ku goge leben ku da abun da kuka guraya, shikenan! Lebe mai laushi da ba’a taba gani ba. Bayan nan, sai ku shafa man kade a leben ku. Sai ku ajiye sauran gaurayan a cikin wani kwano.

Gashi mai lafiya
Kuna fama da amosanin kai? Kuna da goyon bayan mu. Ku zuba baking soda a cikin kwano mai ruwa. Ku jike gashin ku da ruwa sai ku goge gaurayan a fatar kan ku. Ku bar sa na minti biyu, sai kuje ku wanke gashin.

Fuska mai laushi
Man tinya na rage zafin kurajen fuska kuma yana warkar da tabo. Yana saka jiki danshi kuma yana taimakon fata ya girmar da sabon kwayar halitta. Kuyi tambayar shukin tinya (Ana kiran sa Aleo Vera da turanci, ko Alon Erin/Eti Erin da yarbanci, ko kuwa Ibube Agu da Igbo) a ungwan ku. Ku fid da man daga ganyen. Ku shafa shi a fuskan ku sai ku bar sa ya bushe na minti talatin. Sai ku wanke fuskan ku da ruwa mai dumi.

Shikenan! zaku iya samun wadannan sinadaran a gida, a ungwan ku, ko kuwa a kasuwa. Allah ya bada sa’a.

Menene babban sirrin kyawun ku? Muyi labari a wajan sharhi.

Share your feedback